Burin Gwamnatin Kano ta Abdullahi Umar Ganduje ya kasa cika. 

158

- Advertisement -

jahar kano a yau tadau harami domin taron jagoran siyasar Nigeria jagoran talakawa Shugaba mai kishin Al’ummarsa Alhaji Dr. Rabiu Musa Kwankwaso,wanda zai kawo Ziyara jahar Kano a 30/1/2018.

Yanzu haka Al’ummar jahar Kano musamman yan kasuwa da masu sana’ar dinki da masu Sai da jajayen huluna murna harka, domin yanzu haka farar shadda Tayi karanci a kasuwannin jahar Kano bisa Rububin siyanta da akeyi domin tarbar jagoran siyasar Nigeria Dr. Rabiu Musa Kwankwaso. 

A bangare guda kuwa gwamnatin Kano Hankalinta yatashi domin kuwa tasan Al’ummar Kano zasuyi fitar Dango Domin tarbar Kwankwaso inda a yanzu muka jiyo na Hannun Dama ga gwamna Ganduje Yana Furta Munanan Kalamai  ga kwankwaso domin yakawo tarnaki akan zuwan Kwankwaso jahar Kano. 

Amma Abun mamaki kamar yadda kukasan yan kwankwasiyya da Ilimi da Tinani da Sanin yakamata da Bin doka da oda Sunyi Shiru Sunbarshi Yana ta hauragiya.

Kowa yasan wannan na hannun daman Gwamna Ganduje yayi kaurin Suna wajan kawowa jahar Kano tashin hankali ta hanyar Furta kalmomi masu muni ga Abokan adawa.

Gwamnatin jahar Kano dai tanaso yan kwankwasiyya su tanka mata akan kalaman da yaranta keyi domin kawo tsaiko akan wannan Ziyara. 

Hakika anshaida yan kwankwasiyya da hada Babban gangamin taro kuma anshaidasu bisa yadda suke taronsu batare da anzo da sanda ko gora ba,wanda gwamnatin Kano ta yanzu take bakin ciki da Hakan.

Akarshe dai Dan Majalissar Taraiyya mai wakiltar karamar Hukumar Dala Hon. Aliyu Sani Madaki  wanda shima na daya daga cikin jagororin Kwankwasiyya na kasa Mukajiyo shi Yana kara tabbatar da halayyar yan kwankwasiyya na zaman lafiya domin yakara da cewa ziyarar Kwankwaso jahar Kano bata da hadi da neman fitina ga kowa kuma masoyan Kwankwaso Zasu fito cikin kamala su tarbi jagoran talakawan Arewa. 

Inda yakara dacewa duk wani mai kawo tsaiko a wannan Ziyara ko tada fitina Allah yamaida masa Aniyarsa kowaye. 

Kano ta Kwankwaso ce,kwankwasiyya Alherice ga yan Nigeria,Sara da Sassaka Basa Hana gamji To-fo Kwankwaso ikon Allah. 

KR/KN/0007

*@KWANKWASIYYA REPORTERS NIGERIA*

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.