Ganduje Ya Kaddamar Da Aikin Hanyar Kasuwar Kuka Zuwa Kunci

124

- Advertisement -

A kokarin da gwmnatin jihar Kano ke yi na cika alkawarin samar da ga al’uimmomin da ke zaune yankunan karkara don kawo ci gabansu. Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana kudirin gwamnatin ta san a aiwatar da wannan alkawari lokacin da yake kaddamar da aikin hanya mai nisan sama da kilomita 11, wadd ta tashi daga kasuwar Kuka zuwa Sudawa ta hade da babban titin garin Kunci.

Kwamishinan kananan hukumomi ne ya Alhaji Murtala sulan Garo ya wakilci gwamnan wajen kaddamar da aikin hanyar. Gwamnan ya ci gaba da cewa, gwamnatin ta foto da tsari na musamman na karkara salama alaikum da kuma lungu kalkal zai kara mata azama, don ganin duk inda aka fara aiki ba a tsaya ba, har sai an kai gaci, ma’a an karasa aikin kuma an yi bikin budewa.

A wata sabuwa kuma gwamna ya amince da a ci gaba da karatu a babbar makarantar share fagen shiga jami’a wato C. A. S da ke Kunci.

TAn Kaddamar Da Aikin Hanyar Kasuwar Kuka Zuwa Kunciunda farko da yake nasa jawabin shugaban riko na karamar hukumar Kunci Alhaji Alasan Usaini Bakaji Shanono ya yi godiya ga mai giram gwamna da dan majalisar jiha mai wakiltar yankin saboda jajircewa da suka yi don ganin tabbatuwar wannan aiki a inda ya kara gode wa gwaman saboda amincewa da ya yi don dawo da makarantar nan ta CAS don ci gaba da karatu a wannan abin a yaba ne.
Shi ma a nasa jawabin shugaban jam’iyar A.P.C na Kunci Alhaji Rabi’u Ali, cewa ya yi yanzu gwamnatin Ganduje ita take bin su bashi, a inda ya yi alkawarin a zaben 2019 ba sai ya zo neman kuri’a ba su da kansu za su ba shi kuri’a da yake bukata musamman ya bayyana jin dadinsu a kan dawo da makarantar nan, saboda zai rage masu radadin zuwa birni don karo karatu, kuma al’umma za su amfana da ita.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.