Nan Bada Jimawa Ba Ozil Zaiyi Bakunci

124

- Advertisement -

Rahotanni daga kasar Jamus sun bayyana cewa har yanzu mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho, yana zawarcin dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mesut Ozil.

Acikin farkon satin daya gabata ne kungiyar ta Manchester United ta kammala siyan dan wasa Aledis Sanches bayan kungiyoyin biyu sun amince da musayar yan wasan inda Henrikh Mkhitaryan takoma Arsenal.

Sai dai an bayyana cewa Manchester United zata bari har zuwa karshen kakar nan domin daukar dan wasan, mai shekaru 29 a duniya wanda yakoma Arsenal din daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

Kamar Sanches, shima Ozil yaki amincewa da sabon kwantaragin da kungiyar tayi masa tayi sakamakon rashin albashi mai yawa sannan kuma kungiyar bata cin manyan kofuna kamar gasar firimiya da gasar zakarun turai.

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Millan ma tana zawarcin dan wasan sai dai dan wasan yafi son zaman kasar ingila domin cigaba da buga gasar firimiya duk da cewa Arsenal din batason siyar dashi a kasar ta ingila.

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafar ta Arsenal, Mista Arsene Wenger ya bayyana cewa dan wasan yafara tattaunawa da kungiyar domin sabunta kwantaraginsa sanna kuma ya kara da cewa kungiyar tana fatan ganin ta cimma yarjejeniya da dan wasan domin ya cigaba da fafatawa a kungiyar.

Kawo yanzu dai Ozil ya buga wasanni 19 a gasar firimiya inda ya zura kwallaye hudu sanna ya taimaka aka zura kwallaye shida.

Kuyi Share Zuwa WhatsApp Ko Facebook

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.