Real Madrid Ta Bare Mata Da In Dan Wasan Barcelona

106

- Advertisement -

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinedine Zidane ya ce yana jure matsin lambar da yake fuskanta a matsayinsa na mai horar da kungiyar, kuma zai mayar da hankali wajen samun kyakkyawar makoma da kuma yin nasara a gasar zakarun Turai.

Madrid na da tazarar maki 19 tsakaninta da ta daya a teburin La Liga Barcelona, kuma a daren Laraba ne aka fitar da kungiyar a gasar Copa del Rey bayan ta sha kaye a hannun Leganes a karawar da suka yi daren Laraba a filin wasa Bernabeu.

Zidane ya ce, Lokacin da ya fuskanci matsin lamba a matsayina na mai koyarwa, baiyi nadamar komai a kan wasan ba, ko da yake ya dora alhakin akan abun da ya yi,

Ya kara da cewa,Ba su yi amfani da salon da ya dace ba a farkon wasan, kuma hakan ne ya bashi haushi. Bai fahimci abin da yake faruwa ba.

Sai dai yace a yanzu dole zai dage sosai domin ganin sun mayar da hankali a gasar zakarun turai domin ita kadai ce hanyar da zasu mayar da hankali domin samun lashe wata gasa a wannan kakar

A yau dai Real Madrid zata kai ziyara domin fafata wad a kungiyar Balencia a gasar laliga yayinda take mataki na hudu.

Real Madrid Ta Hakura Sai Wata Shekara.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.