Wasu ‘Yan Damfara Sun Gane Kuren Su

106

- Advertisement -

Wasu ‘yan damfarar jama’a masu suna Musa Ahmed mai shekara 39 Sadik Muhammad sun fada tarkon ‘yan sandan jihar Bauchi biyo bayan damfarar wani mutum mai suna Gaddafi Isiyaku kudi da suka yi, inda suka yi masa alkawarin cewar za su mallakar masa da tsabar kudi har naira miliyan 20, gabanin ya ba su kudi.

‘Yan sandan sun yi nasarar kama su ne ta hanyar amfani da dabarun kwararru na hukumar inda hakan ta kai su ga cakumo miyagun, haka zalika sun gabatar wa manema labaru masu laifin domin tambayarsu yadda suke yi wajen damfarar jama’a.

Daya daga cikin mutum biyu da aka kama bisa zargin damfara da zamba cikin amincin ya bayyana wa manema labaru yadda suke yi da kuma yadda aka yi “Sunana Musa Ahmad mazaunin unguwar Dawaki, Mun dan yi wayo ne ma wani na cewar za mu yi masa kudi, a kan za mu karbi kudinsa amma Allah bai yi ba; mun dai karbi dubu 24 a hanunsa, daga bisani ta tashi mana aka kama mu”. A cewarsa.

Ya ci gaba da bayanin cewa “Mun tattauna da shi kan cewar za mu yi masa miliyan ashirin, idan ya ba mu dubu ashirin, kowace miliyan daya tana daidai da dubu daya ke nan, shi kuma ya ba mu dubu 24 ne”. A cewar Musa.

Ya bayyana da bakinsa kan cewar ya taba yin wannan sana’ar ta damfarar jama’a da sunan zai sauya musu kudi mai yawa da zarar suka ba su kadan gaskiya, su kuma sai su ba su na ta karya “Yadda muke yi dai shi ne, bola ce muke kullawa a cikin jaka sai mu bai wa mutum da sunan kudi ne. shi ma wadda muka yi masa wannan har aka kama mu, shi ne mun tara masa miliyan 20 a cikin jakar nan ga shi a gabana, ya dauka ya tafi da ita gida da zimmar tsabar kudi ne har miliyan ashirin a ciki, bai san tarin bola ba ce muka shirya”.

Musa ya kara da cewa “A lokacin da muka bai wa mutum jakar ba zai bude ba ai, dokar ke nan sai ka je gida kawai sai ka ga tulin shara ne muka jera kai ka dauka kudi ne”.

Musa mai shekaru 39 a duniya ya kuma bayyana yadda aka yi har ya tsunduma cikin wannan sana’ar ta zamba a cikin aminci, ya ce “Abun da ya sa na tsunduma cikin wannan sana’ar gaskiya ni ma an taba yi min ne sai ni ma na rama. A da baya ina sana’ata na saida kayan mata da zanin ganin gado, da aka yi min jarina ya karye, kuma ina da yara shi ne ni ma na ke son na rama, to Allah bai yi ba, amma a kan wannan ne na fara, amma ni an karbe min kudi har naira dubu dari uku da hamsin da cewar za a ba ni miliyan 20, yadda aka yi na koya ke nan”. A cewarsa.

Shi ma dayan abokin cin burminsa mai suna Abubakar Sadik ya bayyana cewar an taba yi masa ne kuma ya zo neman hanyoyin ramawa “A da baya ni mai sanar dinki ne ‘tela’, a gaskiyar magana ni na tsunduma wannan sana’ar ne bayan da aka yi min sai nima na shiga domin na rama, wasu sun damfare ni suka kwashe min kekunan dinkina. Wannan dalilin ne ya sa na yi da na yi kuma sai aka kama ni”.

“Ni ina da mata, da yara biyu kuma ni mazaunin unguwar Jahun ne a cikin garin Bauchi. A waya ne muka ga ana yi sai muka koya, wannan shi ne kawai”. A ta bakinsa.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ya yi mana karin bayani kan yadda suka kama masu sane da kuma zamba cikin amincin “A ranar 18/01/2018 ne muka yi nasarar kama wasu mutane biyu Sadik Mohammad 30 da ke unguwar Jahun da Musa Ahmad mai shekaru 39 da ke Gwallagan Mayaka, Bauchi a lokacin da suka damfari wani mutum mai suna Gaddafi Isiyaku a ranar 16/1/2018 kudi har naira dubu 46”.

Ya kara da cewa “sun bukaci ya je wani waje ya ajiye kudin daga bisani za su saura masa ita da naira miliyan ashirin da biyar”. A cewar DSP.

Datti ya ce sun yi nasarar kamosu ne bayan da kwararrun ma’aikatansu na sashin musamman na SIB suka himmatu domin kama miyagum masu irin wannan sana’ar ta wayar tarho, inda suke neman jama’a suna tattaunawa das u da sunan za su zamar da su masu arziki a lokaci guda.

DSP ya ce sun kwato kudi naira dubu 20 daga hanun masu damfarar, da sauran wasu abubuwan da suka kamon.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.