‘Yan Sanda Sunyima Kwankwaso Magiya Zuwansa Kano

113

- Advertisement -

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta nemi haramta wa Sanata Rabi’u Musa kwankwaso ziyarar da ya shirya zuwa Kano, ranar 30 ga watan Janairun nan da muke ciki.

Kodayake rundunar ba ta fito kai tsaye ta ce sanatan kar ya shiga kanon ba sai dai ta nuna amtsayin shawara ce domin hakan ne zai sa a kauce wa rikici a jihar.

Haka kuma rundunar ta ci gaba da cewa, jami’an tsaro za su yi aikinsu na daukar matakin hana barkewar tarzoma matukar suna tunanin hakan na iya faruwa.

Ita dai wannan ziyara da Kwankwaso ya yi niyyar kai wa Kano ta haifar da maganganu da yawa, daga bangaren Kwankwaso da na Gwamna Abdullahi Ganduje wanda ke zargin juna da kokarin haddasa fitina.

Kwamishinan ’yan sanda Rabi’u Yusuf, ya ce jami’an tsaro ba za su zuba ido su ga ana karya doka haka kawai ba tare da sun kai jiki sun kwantar da tarzoma ba.

“Mun samu rahoton da ke nuna cewa akwai tsananin tsoro a zukatan jama’a, ganin yadda garin ya rigaya ya dau zafi.

Wannan shi ne dalili ya sa muke shawartar Kwankwaso da ya soke wannan ziyara da zai kawo.” Inji Kwamishinan ’Yan sanda Yusuf.

“Duk da cewa Sanata Kwankwaso kamar sauran jama’a na da ’yancin yin tarukansu kamar yadda tsarin mulkin kasar nan ya tanada, to amma rahotanni na cike da nuna cewa komai na iya faruwa a yayin wannan ziyara.”

A kan haka ne ya ce ya kamata a soke ziyarar, domin a wanzan da zaman lafiya a Kano, gudun kada bata-gari su yi amfani da ziyarar su hargitsa Kano.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa, da cewa ranar Alhamis, 25 Ga Janairu ya samu wasikar sanar da ziyarar da Kwankwaso zai kai Kano.

Sai jim kadan da bayar da wannan sanarwar sai sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya mayar da martini ga rundunar ‘yansandan wan ya ce sai ya shiga Kanon duk da kokarin da rundunar ke na nuna hatsarin ziyarar tasa.

Byanin haka ya fifo ne ta bakin mai Magana da yawunsa a kan harkokin yada labarai Binta Sipiki. Kwankwasan y ace babu wanda ya isa ya hana shi zuwa Kano domin kao wa ‘yan’uwa da abokan arziki ziyara.

Sai Ya Ke Nan Wannan Lamarin Zai Kasance Haka.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.