Da Alamun: Liberpool Zatatyi Asarar ’Yan Wasanta

116

- Advertisement -

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liberpool, Steben Gerard, ya ja kunnen kungiyar ta Liberpool da kar ta kuskura ta dinga siyar day an wasan ta indai har kungiyar tanason tacigaba da zama babbar kungiya a duniya

Carragher tsohon mai tsaron bayan Liberpool din da kasar ingila ya ce bai kamata dan kwallon kungiyar Coutinho, yabar kungiyar ta Liberpool a yanzu ba, saboda yakamata ace kungiyar tana rike manyan yan wasa.

Wasu rahotanni na cewa Muhammad Salah yana fatan ya koma Real Madrid da buga wasa a kakar wasa mai zuwa, inda har wasu ke cewa ya gama amincewa da wakilan kungiyar ta Real Madrid.

Rahotanni daga Spaniya na cewa Real Madrid za ta sake taya dan kwallon na Masar a watan Yulin shekarar nan, sai dai Liberpool ta ce har yanzu babu wata kungiya da ta mika mata bukatar hakan.

Barcelona ta taya Coutinho har karo uku a lokacin bazara, inda Liberpool ta ki sallama tayin da ta yi kuma tace dan wasan bana siyarwa bane sai a karshe Liberpool din ta amince da cinikin.

Carraghar yace bai kamata kungiya tazama karamar kungiya ba tana siyar da manyan wasanra inda yace yakamata kungiyar tayi koyi da kungiyar Manchester United a wajen siyar day an wasa.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.