Dan Kwambo Ya Samu Kwarin Guiwar Tsayawa Takara

127

- Advertisement -

Labari aga ( Ml Musa Kaduna ) Ya Ruwaito Cewa.

Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Dankwambo ya samu karfin guiwar tsayawa takarar shugabancin kasar nan a karkashin tutar PDP bayan da gamayyar kungiyar matasan Arewa ta fito fili ta marasa baya.

Gamayyar kungiyar matasan Arewan( Arewa Youths Coalition) ta yi kira ga tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar da Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido da kuma Tsohon Gwamnan Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi kan cewa dukkanin su sun janyewa Dankwambo don shi ya fi cancanta ya fafata da Shugaba Buhari.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.