Mafi Akasari Finafinan Hausa Ne, Ke Sanya Ma’aurata Na Kashe Rayuka

120

- Advertisement -

Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano a karkashin jagorancin Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallahu) ta bayyana cewa, yawaitar finafinan Hausa na fadace-fadace ne ya janyo matasa da ma’aurata ke kashe rayuka ba-ji-ba-gani a tsakankanin al’umma.

Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika, wacce hukumar ta aike wa da furodusan fim din Auren Kaddara, Abdul Amart, mai lamba CB/ADM/497/BOL.I mai kwanan wata 17 ga Janairu, 2018.

Ita dai wannan wasika, wacce wakilinmu ya mallaki kwafi, ta na dauke da sa-hannun daraktan kula da sashen shiryawa da bunkasa finafinai na hukumar, Idris Musa Hausawa, ne a madadin Babban Daraktan hukumar, Alhaji Isma’il Afakallahu.

Hukumar ta aike da takardar ne sakamakon zargin sakin tallan wannan fim mai suna Auren Kaddara a kafafen sadarwa na ‘social media’ gabanin hukumar ta amince da ita ko bayar da izinin yin amfani da tallan. Don haka hukumar ta yanke shawarar kin duba tallan bakidaya tare da umartar Furodusa Abdul da ya kawo fim din kacokam, domin dubawa.

A saki na biyu na wasikar, Alhaji Afakallahun ya nanata cewa, “wannan ya zama wajibi ne bisa la’akari da yadda babu kakkautawa a ke shirya finafinan Hausa na fadace-fadace da a ke sarrafa makaman inda matasa da ma’aurata ke kwaikwayo ta yadda hakan ke kai wa ga asarar rayuka.”

Daga nan sai hukumar ta ja kunnen furodusan da ya sanar da dukkan masu ruwa da tsaki cewa, “duk wanda ya daddara ya saka wannan talla ba tare da takardar shaida ba, hukumar ba za ta saurari fim din ba kuma ya zargi kansa.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.