Na Cin Cinta A Zabeni A Matsayin Dan Takara Inji Atiku Abubakar

128

- Advertisement -

Ganin yadda mutanen Nijeriya suka shiga mawuyacin halin matsalar tattalin arziki wanda ya haifar musu da fatara da rashin samun ingantaccen abinci da sauran matsalolin rayuwa, a daidai wannan lokaci ne jama’a suka himmatu wajen ganin sun samu sabbin shugabannin da za su ja ragamar kasar nan ta hanyar lura da irin mawuyacin halin da mutane ke ciki domin ganin an ceto su ta hanyar inganta rayuwa da samar da aikin yi da lura da ilmi da kiwon lafiya da samar da shirin gaskiya don inganta noma.

Wannan lokaci ne da ya kamata mutane su himmatu wajen lura da wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jama’ar Nijeriya ta hanyar lura da irin matsalolin da suke ciki da nufin magance musu. A saboda haka daidai wannan lokaci, ganin yadda a baya mutane suka sa zaton ganin shugabannin da ke mulki a halin yanzu a Nijeriya za su iya fitar musu kitse a wuta amma lamarin ya zamo ba inda suka zata ba. Don haka a daidai wannan lokaci ne tunanin ‘yan Nijeriya ya koma ga neman mutanen da suka taka rawar gani a baya wajen ciyar da kasa gaba ta hanyar lura da irin tausayin da suke da shi da nuna sanin yakamata. Inda a halin yanzu dan Nijeriya ke neman mai cetonsa daga irin mawuyacin halin da ya shiga na matsin tattalin arziki.

Mutane da dama suna fitowa wajen takara domin neman shugabannin kwarai da za su fitar musu da kitse a wuta, amma ganin irin wahalar da suka sha a baya kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, shi ya sa yanzu jama’a da dama suka natsu wajen ganin sun auna irin taimakon da mutane suka yi a baya kafin idan sun fito a kai ga zabar su a matsayin ‘yan takara don samun masu share musu hawaye.

Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya a lokacin shugaban kasa Obasanjo ya taka muhimmiyar rawa wajen bayar da wakilcin da ya kamata a matsayinsa na dan Arewa wanda ke wakiltar mutanen Arewa a wancan lokacin. Don haka jama’ar Arewacin Nijeriya a halin yanzu ke yin dubi game da irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban Nijeriya a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa, inda ya kafa mutane da dama kuma ya samar da hanyoyin da mutane za su amfana da arzikin da Allah ya yi masa ta hanyar bude kafafen watsa labarai da kamfanonin samar da ruwan sha da lemon kwalba da kuma bude makarantu da sauran su inda kowa ya ga rawar da ya taka a matsayinsa na dan Arewa.

Abin da Atiku Abubakar ya yi duk domin gina Arewa ya yi su, kuma za a ci gaba da cin moriyar su har duniya ta tashi. Don haka mutane ke ganin a yanzu ya cancanci yabo da kuma fitowa a goya masa baya don ya samu shugabancin Nijeriya ta yadda zai kwato mutane daga wahalar da suka shiga, musamman a wannan lokaci da ba wanda ya zaci dan Nijeriya zai nemi abin da zai ci ya rasa amma yanzu an wayi gari talauci ya haifar da cututtuka da lalacewar tarbiyya da matsaloli masu yawa.

Atiku Abubakar shi kadai a Nijeriya wanda tun yana mataimakin shugaba Obasanjo ya rika fitowa fili yana kalubalantar manufofin da za su shigar da talakan Nijeriya cikin wahala. Kuma bayan gama waccan gwamnati yanzu ‘yan Nijeriya sun fahimci gagarumar rawar da ya taka wajen ciyar da Nijeriya gaba. Don haka ya himmatu wajen fitowa takarar shugabancin Nijeriya domin magance matsalolin ‘yan Nijeriya tare da ceto su daga cikin mawuyacin halin da suka shiga. A saboda haka ya zamo wajibi ‘yan Nijeriya su lura da masu kishin kasa da kuma kaunarsu. Saboda duk irin mawuyacin halin da aka shiga Atiku Abubakar bai taba gujewa ya bar ‘yan Nijeriya ba, kuma a kullum shirye yake wajen ganin ya taimaki ‘yan Nijeriya ta yadda za su ci gaba su kuma fita daga irin mawuyacin halin da suke ciki.

Saboda haka yanzu lokaci ne da ya kamata ‘yan Nijeriya su lura da masu kaunarsu na gaskiya ta hanyar yin abin da ya dace don su taimaki kan su ta hanyar taimakawa wadanda ke bukatar fitar da su daga cikin mawuyacin halin da suka shiga. Da fata Allah ya sa mutane su lura su ci gaba da yin addu’a game da samun shugabancin wanda suka damu da damuwarsu, irin su Atiku Abubakar don a kawo karshen irin matsalolin da ‘yan Nijeriya suka abka da nufin samun sauki a baya amma lamarin ya zamanto yaudara da ha’inci da rashin tausayi, da fata Allah ya yi ma na jagora.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.