Wasikar Obasanjo Zuwaga Buhari

130

- Advertisement -

A cikin makon nan ne tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya aike wa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wata muhimmiyar wasika wacce ta tayar da kura a farfajiyar siyasar kasar, inda Obasanjon ya yi kira ga Buhari da kada ya nemi yin tazarce karo na biy a babban zaben kasa mai zuwa na 2019, duk da cewa, shi a lokacinsa a na zargin ya nemi ya bankara kundin tsarin mulkin kasar, don yin tazarce karo na uku, alhali mafi yawan ’yan kasar ba su gamsu da yadda ya ke tafiyar da mulkin kasar a wancan lokacin ba.

Bugu da kari, Obasanjo na daga cikin wadanda su ka mara wa Buhari baya ya dare karagar mulki a 2015. To, amma ta fuskar mulkin Buharin, da yawa na nuna damuwa kan halin matsin aljihu da a ka shiga a fadin kasar.

Shin Obasanjo fargar jaji ya yi a kan Buhari ko kuwa kissar siyasa ya ke son nunawa? Mene ne ra’ayinku? Za mu wallafa wasu daga cikin ra’ayoyinku a mako mai zuwa in sha Allahu. A tabbata an yi rubutu mai inganci ba tare da cin zarafi ba.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.