Yau CE Ranar Murnar Zagayowar Haihuwa Nafisa Abdullahi

161

- Advertisement -

Manyan masu ruwa da tsaki a harkar fina-finai hausa na masana’antar Kannywood sun halarci walimar taya murnar zagoyawar ranar haihuwar jaruma Nafisa Abdullahi.

A ranar laraba 24 ga watan janairu ne jarumar ta cika shekara 27 a duniya.

Domin nuna farin cikin zagoyowar wannan muhimmin ranar a rayuwar ta ta hada wata walima ta musamman wanda har ta gayyaci kawaye da abokan huldar ta a masana’antar kannywood.
Anyi wannan sharholiyar a dakin cin habinci na bristol palace hotel dake Kano.

Manya baki da suka halarci wajen walimar sun hada da shugaban hukumar tace fina-finai na jihar kano  Alhaji Ismail Na’abba Afakallah da masu shirya fina-finai Aminu Saira da Nazir Dan hajiya.

Suma jarumai Maryam Booth da dan uwanta
Ramadan Booth w anda ranar haihuwar shi ya zo daidai da na mai biki  sun halarci taron.

Sauran baki sun kama da mawaki Nazir Ahmad (Sarkin waka) da Maryam Yahya da Sanusi Oscar.

Allah ya Bada Za’a

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.