An Fanin Bebin Roba Domin Samun Gamsuwa Ga Samari Da ‘Yan Mata

155

- Advertisement -

A Yanzu An samar da bebin roba don biyan bukatar samari da ma ‘yan mata Yar tsanar na aiki da batir, wasunsu ma suna rawa da magana

Akwai mata akwai maza, akwai yara akwai manya, akwai turawa akwai bakaken fata Zamani ina zaka damu! A wannan shekaru dai sabon salo a kasashen duniya shine na samar da bebin roba masu aiki da batura domin biya wa wadanda basu da iyali bukata ta sha’awa. Ana sayar da bebin robar ne dala dubu biyu, kusan naira 700,000 kenan.

Ita dai bebin robar akwai fara akwai baka, akwai ma masu rawa da duk wana siga ta motsa shawa’a, kuma a kowacce kasa ana iya oda a samu.

Sai dai kuma al’adu a kasashen musulmi da ma na masu ra’ayin mazan jiya ba lallai su bari ba.

Akwai dai batu na abin-da-hannun daman-ka ya mallaka, ko bebin roba zata iya shiga wannan layin, sai anyi fatawa da fashin baki sannan zamu gane.

A yanzu dai wasu matan Najeriya sun bazama shafukan sada zumunta na facebook suna baza ra’ayoyinsu, suna cewa ragwancin maza ne a ce sun koma bin roba saboda gudun saya wa mace kayan shafe-shafe da na kwalam.

Su kuwa samari sarakan zumudi, sun ce sun huta da fada, da list na kayan saye, da sayan katin waya, da ma kuma tsoron ko ana yaudararsu ne.

Allah Ya Kiyaye Mu Da Wannan Sabon Al’amari Domin Duk Laifine Amfani Da It’s Ga Musulmi.,

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.