Dan Aikin Gida Ya Zama Sanadiyar Mutuwar Mai Gida ( Yayinda Uwar Gida Ke Lalata Da Shi )

108

- Advertisement -

An bayar da labarin cewa ma’auratan wadanda Inyamuarai ne dake gudanar da kasuwanci a Yaunde ta kasar Cameroon, sun fara samun sabani ne tun daga lokacin da mijin ya fara zargin akwai alakar iskanci tsakanin matarsa da wani yaron kantinsa.

Ugochukwu Okeke ya dinga kafa tarko har yayi sa’ar kama matar tasa mai suna Chinenye Okeke tare da yaronsa suna aikata zina a cikin gidansa, a yinkurin sa na daukar mataki ne matar tasa tare da saurayinta suka hallaka shi sannan suka lullube shi da bargo sukayi sakashi a mota da niyar su je su jefar da shi.

Asirin su ya tuno ne lokacin da wani dan sanda ya hango alamar jini na fita daga cikin motar, bayan tsayar da su aka bincika motar sai ga gawar mamacin.

Yanzu haka suna hannun hukumomin birnin Yaunde dake kasar ta Kamaru Allah Ya Tsaremu Ameen.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.