Sama Da Kungiya 36 Na Matasa Sun Nemi Buhari Kar Ya Yi Takara

114

- Advertisement -

Wasu kungiyoyin matasa guda 36 da sukayi taro a Kano sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari akan kar ya nemi sake tsayawa takarar shugabancin kasarnan a karo na biyu duba da gazawarda Gwamnatinsa tayi wajen biyan bukatunda aka zazeta akai .

Shugaban Kungiyar Malam Abdumajid Babangida

ya bayyana hakan a taron manema labarai da suka gudanar a Kano. Ya ce duk da cewa shugaban kasar ya karbu a wajen al’umma amma sai gashi ana yi musu gashin kuma a Gwamnatinsa.

Ya ce duk wanda ka ji yana cewa Buhari ya ci gaba ba zai ce maka an sami nasara da ake zato za a samu ba, duk masu wannan hankoro na ya ci gaba suna yi ne kawai saboda biyan bukatun kansu suna dodorido da Buhari.

Kwamared Abdulmalik Babangida ya ce baya ga matsalar yan ta’adda akwai rikicin kabilanci dake fuskantar sassan kasar nan da rikicin manoma da makiyaya da barazanar ’yan aware.

Ya musanta cewa wannan kira da suke sa su aka yi da cewa suna iya kokarin su ne wajen wayar da kan Buhari ya fuskanci halin da al’umma ke ciki, su na taro ne ba don wasu ba.

Kwamared Abdulmaji ya ce su din nan a baya tun Buhari bai shiga wata jam’iyya ba, sun yi tattaki sun je sun same shi suka ce suna bukatarsa ya zo ya ceci kasar nan. “Ya sani, ya samu aiki a baya mun yi masa yaki tun bai shiga wata jam’iyya ba, har ya zo ya shiga jam’iyyu yake takara har sai karo na hudu Allah ya bashi nasara, amma abin mamaki bayan kafa Gwamnati muka fahimci Gwamnatin bata da wani tsari na kawo sauki na matsaloli yan kasa ke fuskanta”

Ya ce duk da yayi kokari wajen yakar boko haram, amma akwai matsaloli na rashin ayyukan yi wanda ya jawo yawaitan matasa a shaye-shaye da shiga matsaloli iri-iri ko rigingimu na kabilanci ga shi ba magunguna a asibiti, harkar ilimi ya tabarbarewa abubuwa suna ta lalacewa, yan kasa suna cikin tagayyara ba karama ba.

Kwamared Abdulmajid ya ce suna shawartar Buhari da kar ya yarda masu bukatar babakere a sha’anin Gwamnati su zuga shi ya sake tsayawa takara a 2019.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.