Sama Da Mutane 100 Sanadiya Hari Da Aka Kai A Najeriya

139

- Advertisement -

Kusan mutum dari daya ne suka mutu a hare-haren da aka kai a sassan Najeriya daban-daban tun daga ranar karshe ta 2017 zuwa karshen makon jiya.
Idan muka soma daga jihar Ribas da ke kudu maso kudancin kasar, ‘yan bindiga sun kashe mutum 23 bayan sun fito daga coci inda suka je addu’o’in murnar sabuwar shekara.

Lamarin ya abku ne a garin Omoku da ke karamar hukumar Ogba-Egbema-Ndoni, mai nisan kilomita 85 daga birnin Fatakwal, babban birnin jihar.

Rundunar ‘yan sandan jihar dai ta tabbatar wa BBC da abkuwar lamarin.

Wasu rahotanni na cewa harin yana da nasaba da rigingimu da ake yi tsakanin wasu gungu da ba sa ga maciji da juna a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur.

Kuma a ranar Lahadi ne Runduna ta Shida ta sojojin kasa a Najeriyar da ke Fatakwal ta ce ta kashe mutumin da ake zargi da hannu a kisan mutanen.

A wata sanarwar da mai magana da yawunta Kanar Aminu Iliyasu ya fitar, rundunar ta ce ta samu sahihin bayani ne daga mutanen gari game da maboyar Don Waney, wanda ake zargi da kitsa harin.

Benue

Kazalika a dai ranar karshe ta shekarar 2017, wasu mutane da ake zargi Fulani makiyaya ne suka soma kai hari a wasu kauyuka na jihar

Gwamnatin jihar ta Benue dai ta ce an kashe akalla mutum 33 a hare-haren da aka kai kauyukan jihar da ke karamar hukumar Guma, mahaifar gwamnan jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Lawrence Onoja, wanda ya tabbatar wa BBC adadin mutanen da aka kashe, ya kara da cewa an fara kai hare-haren ne ranar karshe ta shekarar da ta gabata kuma aka ci gaba da kai wa har zuwa safiyar Talata ta makon jiya.

Sai dai kungiyar Miyetti Allah ta bakin shugabanta Ubbi Haruna ta shaida wa BBC cewa ba Fulani makiyaya ne suka kai harin ba, tana mai zargin gwamnatin jihar da kashe Fulanin da ke kan hanyarsu ta ficewa daga jihar a lokacin.

Hare-haren da aka kai a Rivers da Benue sun sa ‘yan kasar, musamman masu amfani da shafukan sada zumunta, sun yi ta sukar gwamnatin tarayya.

Shugaba Muhammadu Buhari dai ya bayyana takaicinsa kan lamarin sannan ya umarci Babban Sufeton ‘yan sandan kasar ya karfafa tsaro a yankunan.

Hakan ne ma ya sa aka aike da manyan jami’an rundunar ‘yan sanda jihohin domin su wanzar da zaman lafiya.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.