An Yiwa Jaririya ‘Yar Wata 8 Fyade A Indiya ( Rayuwa T Chanza

134

- Advertisement -

An yi wa wata jaririya ‘yar wata takwas fyade a Delhi babban birnin Indiya, inda ake zargin wani dan uwanta, abokin wasanta ne ya yi mata.

Rahotanni sun ce a yanzu haka yarinyar tana cikin mawuyacin halin a asibitin da aka kai ta bayan da ta samu munanan raunuka a ranar Lahadi. ‘Yan sanda sun shaida wa manema labarai cewa sun kama matashin da ake zargi da aikata laifin mai shekara 28.

Kwamishinar kula da al’amuran mata ta Delhi wati Maliwal, wacce ta ziyarci jaririyar a asibiti ranar Litinin da daddare, ta bayyana irin raunukan da ta gani a jikin yarinyar da cewa abun tsoro ne matuka.

Al’amarin ya faru ne a ranar Lahadi, amma sai a ranar Litinin ne kafofin yada labarai suka samu labarin.

Ms Maliwal ta aika da sakon Twitter cewa, sai da aka yi wa yarinyar tiyata ta tsawon sa’a uku.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.