Amurka Ta Zargi Koriya Ta Arewa Da Yi Mata Kutse Akan Hanyar Sadarwarta

91

- Advertisement -

A ranar Talatar data gabata ne, Kasar Amurka ta sanar da cewar, Koriya ta Arewa itace hummul haba’insin akan yawan yin kutse akan hanyar sadarwa da zata iya zama illa ga kasashe dari da hamsin a duniya.

A taron manema labarai da mai bayar da shawara akan harkar tsaro na fadar kasar ta Amurka Tom Bossert ya kira yace, “sakamakon binciken da aka gudanar a tsanake, kasar ta Amurka ta danganta kutsen na `Wannacry’ akan Koriya ta Arewa.”

Ya bayyana cewar, a bisa hanyoyin da hukumomin tsaro na kasar Amurka suka bi, ya tabbatar da cewar kutsen gwamnatin Koriya ta Arewa ce ta aiwatar dashi kai tsaye ga Amurka, da kuma ta hanyar irin kutsen da

kasar ta kai a madadin Pyongyang.

Yace kutsen, na da kasar ta Koriya ta Arewa ta kai na “ransomware’’ wanda ya lalata (Microsoft Windows) wanda shine tsarin da akafi yin amfani dashi a duniya.

Bossert ya soki Koriya ta Arewar akan kutsen data kai a shekaru da dama da suka shude.

A cewar Bossert “ wannan nuna dabi’ar ta mugunta, tana kara zamowa barazana.’’

Bossert ya yi kira ga daukacin duniya dasu zargi Koriya ta Arewa akan wannan halin da kuma yin kira da’a hada karfi da karfe wajen samar da hadin kai a tsakanin kasashen duniya don samar da kyakyawan tsaro akan

kai hari a kafar yanar gizo.

A cewar sa, gwamnatin kasar Amurka zata jagoranci wannan kokarin da daukar mataki na gaggawa daga (Microsoft) da shafin sada zumunta na (Facebook) data sauran kamfanoni na na kimiyya wadanda zasu taimaka a tarwatsa kutsen na kasar Koriya ta Arewa da kuma ta hanyar yin amfani da shirin kasar Amurka na tarwatsa kwayoyin Wannacry da kuma taimakawa wajen ragewa kutsen na Wannacry gudu.

A cewar sa, “a lokaci ma zuwa zamuci nasara akan hakan, amma sakamakon wadanda harin na ransomware, ya shafe su, ta hanyar rufe masu na’urorin masu kwakwalwa, aiki ne ja kuma zaici kudi mai yawa.

A karshe Bossert ya ce, “wannan kutse ne na dabbanci’’.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.