An Gargadi ’Yan Siyasa Da Su Guji Kalaman Batanci

91

- Advertisement -

Shugaban wata kugiya mai zaman kanta da ake kira “Rights Without Biolence” Dakta Ahmad Jibrin Suleiman ya gargadi ‘yansiyasa da su guji ruwa wutan rikicin da ke tsakanin fulani makiyaya da Manoma. Ya yi wannan gargadin ne a taron manema labarai da ya kira a ofishinsa da ke Zariya,ya ce, “Ba zamu zura ido muna kallo wasu ‘yan tsiraru su tarwatsa mana kasa ba”. Dakta Suleiman ya nuna damuwarsa a kan kalaman da suka fito daga kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) da kuma kungiyar Jama’au Nasril Ilam (JNI) “Kalamai ne da zai iya haddasa rikici a kasar nan, ya kamata a rinka kalaman da zasu haba kan alumma a duk lokacin da rikici ya taso”.

Kungiyar ta ce, an dade ana zubar da jinin ‘yankasa a rikice-rikicen da ke aukuwa da sunan makiyaya da manoma, saboda haka, ya kamata gwamnatin tarayya ta hukunta jami’in tsaro a duk lokacin da wani dan kasa ya rasa ransa, hakan zai sa jam’an tsaronmu su dauki kare rayuwar ‘yankasa da mahimmanci, wadanda kuma aka samu da laifin halaka wani dan Nijeriya ya kamata a tabbatar da doka ta yi halinta ta hanyar hukunta shi yadda ya kamata.

“Kada a yarda wata jiha ta horar da ‘yan banga ko ta mallaki jami’an tsaro nata na kanta, wanda aka samu da laifin yin haka a masa hukunci mai tsanani, haka kuma a binciki dokokin hana kiwo da wasu jihohi suka kafa saboda tsananin illar da suke da shi ga tsaron kasa da zamantakewarmu”

“Lokaci ya yi da gwamnati zata kafa kwamitin na musamman da zata binciki kashe-kashen da aka yi na rayukan ‘yan Nijeriya a garuruwan Zango-Kataf da Filato da Tafawa Balewa da Yelwan Shandam da Ibbi da Wukari da Mambila da Adamawa da kuma Zamfara da kuma tabbatar hukunta duk wani mai hannu a kashe-kashen har da jami’an tsaron da sakacinsu ne ya jawo asarar da barnar da aka yi” in ji shi.

Dakta Sulaiman ya kara da cewa,in har an yi maganin matsalar ‘yankasanci da bako a Nijeriya babu dan Nijeriya da zai fukanci wani banbanci a ko ina ya ke zaune a fadin tarayyar kasar nan saboda ba daga nan yake ba.

Ya kuma yaba wa gwamnan jihar Filato Mista Solomon Lallon saboda dattaku da tsoron Allah da ya nuna na kin hada hannu da gwamnonin jihar Binuwai da Taraba wajen kafa dokan hana kiwo.

Ya kuma gargadi tsohon ministan jiragen sama Femi Fani-Kayode da cewa, ya guji kalaman batancin da zai iya hargitsa kasar nan, “Dole mu kare kasar na daga komawa kamar kasashgen irinsu Libya da Sudan ta Kudu da Rwanda da kuma Yugoslabia.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.