Arsenal Ta Tabbatar Da Siyan Aubameyang

115

- Advertisement -

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake kasar faransa ta kammala siyan dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, Peirri-Emeric Aubameyang bayan kungiyoyin biyu sun amince da juna.

Aubameyang, mai shekara 28 a duniya ya sauka a birnin Landan tun ranar Talata domin a gwada lafiyarsa a kungiyar ta Arsenal sannan kuma suka karasa ragowar yarjejeniyar da basu karasa dad an wasan ba.

Shine dan wasa na biyu da kungiyar ta Arsenal ta siya bayan ta dauki Henrikh Mkhitaryan daga kungiyar kwallon kafa ta Manchester United sakamakon musaya da kungiyoyin biyu sukayi da Sanches inda ya koma United din dabuga wasa.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Dortmund ta tabbatar da cinikin inda tace tana yiwa dan wasan fatan alheri a rayuwarsa tan an gaba da zai sake.

Shugaban gudanarwar kungiyar ta Dortmund, Machael Zorc ya bayyana cewa Aubameyang babban dan wasa ne wanda ya taimakawa kungiyar sosai saboda haka bazasu manta da irin gudunmawarsa a kungiyar ba kuma yakafa tarihi a kungiyar har ila yau kuma ya rubuta sunansa a tarihin kungiyar har abada.

Dan wasan dai ya buga wasanni 144 a akungiyar ta Dortmund inda ya zura kwallaye 98 cikin shekaru biyar da yayi a kungiyar sai dai har yanzu ba’a bayyana lambar dad an wasan zai saka a bayansa ba.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.