Ba Zan Hana Ibrahimovic Barin United Ba, In Ji Mourinho

74

- Advertisement -

Mai koyar day an wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho ya ce Manchester United ba za ta hana dan wasan kungiyar, Zlatan Ibrahimovic barin kungiyar ba idan har ya bukaci yin hakan.

Ana alakanta dan wasan mai shekara 36 a duniya, wanda bai buga wasan karshe bakwai na Manchester United ba a bara, sakamakon raunin da ya yi cewar zai koma kasar Amurka da buga wasa a kungiyar Los Angeles Galady.

Ibrahimovic ya tsawaita zamansa a Manchester United zuwa shekara daya a bara, amma wasa bakwai ya buga a kakar bana kawai bayan doguwar jinya dayayi tun a bara.

Mourinho ya ce Zlatan Ibrahimobic yana cikin yarjejeniyar shekarar karshe a kungiyar, amma bai ce masa komai ba kan batun tafiyar tasa amma idan har da gaske ne yana son gwada sa a to ba za su hana shi ba.

Mourinho ya ce Ibrahimobic dan kasar Sweden bai sheda masa cewar yana son barin Manchester United ba saboda haka bazai iya cewa komai akaiba tukunna.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.