Dan Adam Da Siyasar Zub Da Jini (II)

69

- Advertisement -

Kazalika sun yi wuraren da Fulani za su irka ya da zango idan sun gaji, akwai wurin kiwon gida da na makiyaya fulanin tashi, kuma duk an sanya shi taswirar kasar nan, wanda ke son ganin haka sai ya je ma’aikatar noma ya ce a binciko masa zai gani. Amma saboda sakaci na gwamnatoci ana gani wadannan abubuwa suna bacewa, a wasu jihohin namu na arewa ma gwamna da kansa shi yake sayar da irin wadannann wuraren. Ko kuma hukumar kula da filaye su rika yanka wa ana sayarwa ga masu hannu da shuni ko ‘yan jagaliyar siyasa.

Yanzu an zo matsayin da duk wani burtali da shanu za su bi babu shi, idan bafulatani ya koro dabbobinsa sai dai ya bi gefen kwalta, kuma wani lokacin yana cikin tafiya mota ta kashe masa dabba, idan kuma ya sauka daga kwaltar to cikin gonaki shanun za su shiga. Idan za a fito a fadi gaskiya, in an bi ta barawo sai a bi ta mabi sawu. Idan makiyaya suna da laifin shiga gona, to manoma ma suna da nasu laifin, domin abinda dokar kasa ta ce, duk manomi zai ba da tazara tsakanin gonarsa da titi kafa 50. Amma ba a samun haka, idan manomi ya dauko noma baya tsaya wa sai a baki kwailta, kuma wannan wurin da zai bari tazara shi ne muhallin da makiyaya za su bi.

Bafulatani makiyayi bai san zaman gida ba, kai manomi kai ne ake shimfida maka titi, shi sai ya yi tafiyar kilomita 1000 a kasa yana rataye da sandarsa, kai ake ba wa wutar lantarki, shi sai ya kwana a jejin babau ko alamar bukka. Amma wannan duk laifin hukuma ne, ya kamata yadda hukuma take bai wa manoma kulawa, ya zama tana lura da makiyaya, domin yadda manomi ke tinkahon shi dan kasa ne, haka shi ma makiyayi yake ji a ransa.

Amma a yau an sake samo salon a kashe su ba su ji ba ba su gani ba. Rahotanni sun nuna a ‘yan kwanakin nan da su gabata an kashe Fulani a Mombila sun kai mutum 1000, tsakanin mata da kananan yara. Sannan an yanka gami da kashe shanun da yawansu ya kai kimanin 40,000, baya ga kisan da aka yi Adamawa, aka zo jihar Binuwai nan kuma aka samu wasu suna shiga irinta Fulani suna kai wa ‘yan uwansu hari da sunan Fulani ne.

Kazalika runduanar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Binuwai din, ta gabatar da wani gungun ‘yan ta’adda da aka kama dauke da makamai da suka hada da bindiga kirar AK 47, sun kai hari kan ‘yan uwansu da sunan Fulani ne suka yi, amma da aka rika cewa wai ‘ya Bigilante ne, kuma kawo yanzu babu wani rahoto da ya nuna an gurfanar da su gaban kotu. Bugu da kari rundunar ‘yan sandan sun sake gabatarwa da ‘yan jarida wani mutum da sanye da kayan Fulani zai kai hari, wannan ya nuna a fili irin makircin da kutunguilar da ake shirya wa Arewa na kokarin wanzar da tashin hankali a yankin.

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na III, Allah ya kara masa lafiya, ya yi kira ga gwamnatin tarayya kan daukar mataki don kawo karshen lamarin, kazalika ya yi hani da kiran da ake yi wa Fulani’yan ta’adda. Sarikin Kano Muhammadu Sanusi II, Allah ya ja zamaninsa, a cikin hirar da ya yi da ‘yan jarida ya bayyana matukar rashin jin dadinsa da yadda hukuma ta zuba ido ana kasha Fulani.

Ya ce, “Kisan kare dangin da aka yi a Numan shi kansa ya mikawa gwamnatin tarayya wasu hotuna na mutunen da aka kashe, da kuma irin asarar dukiyoyin da aka yi, kai har ma da hotunan masu aikata kisan, da ma sunayen wadan da suke haddasa abin. Amma gwamnati ta yi kunnen uwar shegu da lamarin.

To idan hukuma za ta sa ido ana irin wannan ta’addanci, ba tare da tsawatarwa ta hanyar daukar mataki ba, ta yaya za a samu zaman lafiya.?

Irin wannan yakin ana fara shi kamar da wasa, amma daga karshe ya zo ya addabi mutane, idan ba a manta ba, da irin wannan kisan mummuken rikicin Boko Haram ya fara, ga shi an shafe shekaru jinin al’umma jinin yana zuba, baya ga asarar dukiyoyi. Mu ‘yan arewa da zarar an fara fuskantar irin wannan halin, sai mu rika kallon abin nesa da mu har ma ka ji muna cewa, ai wuri kaza abin ya shafa. Yau ga shi an dauko wata hanyr da za a yi amfani da wasu wadanda ba su da wani amfani cikin al’umma suna afkawa mutanen da suka amince su sha ko wace wahala don neman abin da za su samu rufin asiri, su ake bi ana kashewa, kuma msu kisan nasu bas u da sisin kwabo, kawai ana fake wa ne da manoma ana zalintar su.

A yau dai hankali ya koma kan Fulani, su ke kallo a matsayin wasu mutane kamar ba ‘yan kasar nan ba. Su ake bi ana hallakawa da sun motsa kuma a ce su ne ‘yan ta’adda, idan sun dawo garemu mu tsangwame su, in sun koma wurin da ba jinsun su ba nan kuma suna kallonsu gara dabba da su.

Dole ce ta tilasta wa Fulani daukar makami don kare kansu, idan kowa zai tsinci kansa a halin da suka tsinci kansu, kuma ya ce zuba ido har sai hukuma ta shigo ciki, to ba makawa wannan kabila sai an kare su komai yawansu, domin Hausawa na cewa zara ba ta barin dami.

Amma daga baya me ya faru? Sai wadancan suka rika shiga kafofin yada labarai da shafukan sada zumunta suna yada hotuna na daukar fansa da Fulani suka yi. Ai mutum in ba mahaukaci ba ne, a ce ku yi kungiya ku shiga garin mutane ku halaka sama da mutum 1000, kuma a ce ka je gida ka yi bacci lafiya lau, kai ma ka san wannan ka cika jahili na sara da gatari.

Muna kira ga hukumomin da abin day a shafa das u dauki matakin dakile wannan ta’addanci, matukar dai sun yi amanna al’umma suke mulka da nufin kare masu jininsu da dukiyoyinsu. Allah ya ga bamu zama lafiya a kasarmu.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.