DAN TALAKA, KAI BA JAKI BA KUMA KAI BA MANGALA BA

160

- Advertisement -

DAN TALAKA, KAI BA JAKI BA KUMA KAI BA MANGALA BA

Ahirr dinka wallahi da rikicin siyasar Kano.

Inaso duk ‘dan talaka da yake yin sara-suka saboda ‘yan siyasa ya amsa wadannan tambayoyin guda goma sha biyar :-

1. Menene ribar da ka samu tsawon lokacin da kayi a cikin jagaliyar siyasa?

2. Wai ka taba zuwa Abuja kaga rayuwar da sukeyi da su da ‘ya’yansu?

3. Shin sun ta6a tunanin mayar da kai makaranta?

4. Kafi ‘ya’yansu sonsu ne da bazasu fito ba ayi arangama dasu ba?

5. Dama Allah ya halicceka ne don ka bautawa wani?

6. Wani a cikinsu ya taba yi maka nasiha akan ibada ko rayuwarka?

7. Kana tunanin makomar rayuwar gidanku kuwa?

8. Ka gane cewa basu da buqatarka sai za6e yazo?

9. Kana da gado ne a cikin dukiyarsu?

10. Ka cire rai da arziki ne kai?

11. Baka sha’awar ka hau kujerar da suke kai?

12. Kasan kuwa suna sane suka barka da jahilci?

13. Kana iya cin lafiyayyen abinci sau uku a kowacce rana?

14. Ka ta6a tunanin cewa kullum qara tsufa kakeyi su kuma qara samun duniya suke?

15. Ka yadda cewa *Sulen Kudi Direban Waka 🗣🎙* talaka ne  Kuma masoyinka?

Wadannan tambayoyin guda goma sha biyar sun isheka kayiwa kanka hisabi, zaka gane hadarin da rayuwarka ta dosa.Mafi munin abun shine kai dai ba karatu bane da kai balle su baka AIKI kuma kai ba nutsuwa bace da kai balle su baka KWANGILA ko JARI.Kaga ka zama kai ba JAKI ba kai kuma ba MANGALA ba.

Allah ya shiryar damu.

Amin S Amin

Sin…..✍   (By) Sulen Kudi Direban Waka

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.