INEC Za Ta Bayyana Sakamakon Zaben 2019 Ta Na’ura Mai Kwakwalwa

86

- Advertisement -

Hukumar zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa, zata bayar da sakamakon zaben da zai gudana a shekarar 2019 a rubuce ta hannun wakilan jam’iyyu za kuma sanar da sakamakon zaben ta na’ura mai kwakwalwa, saboda haka Hukumar ta bukaci Hukumar NCC da ke samar harkokin sadarwa a kasar nan su taimaka musu.

Shugaban na INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya mika wannan bukatar ne lokacin da ya ziyarci shugaban Hukumar sadarwa ta kasa NCC Farfesa Umar Danbatta a ofishinsa dake Abuja ranar Talata.

Ya ce, wannan tsarin ne za a yi amfani da shi a zaben da za a gudanar a jihohin Ekiti da Osun a watannin Yuli da Satumba na wannan shekaran.

Yakubu ya kara da cewa, “Muna shirin yin amfani da na’ura mai kwakwalwa a zaben da zai gudana a jihohin Ekiti da Osun sannan daga baya zamu yi amfani da na’uran a zaben gama gari da zai gudana a fadin kasar baki daya.

“INEC ta shirya yin amfani da na’ura mai kwakwalwa saboda haka zata dogara da kanfanonin sadarwa domin tura sakonnin da za a tattaro daga mazabu domin watsawa zuwa jama’a”

Yakubu ya kara kira ga Hukumar NCC da ta shirya taro tsakaninta da kanfanonin sadarwa domin tattauna yadda zasu taimaka wa INEC a yayin gabata da zaben shekara 2019.

Shugaban INEC ya kara da cewa, “Sannan muna bukatar NCC ta taimaka mana domin samun goyon bayan kanfanonin sadarwa ta yadda za a samu nasarar aikin zaben da zai gudana abin da muke bukata a halin yanzu shi ne yadda za a ilimantar da masu jefa kuri’a da masu ruwa da tsaki a harkar zaben”

“Muna son fito da taswirara amfani da na’ura mai kwakwalwa wajen tuwa sakonni ta rubuta da murya da kuma yadda masu jefa kuri’a zasu gano in da runfar zabe yake da kuma inda masu jefa kuri’a zasu karbi katin zabensu, gaba daya fito da tsarin da za a samu gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali”

A nasa jawabin, shugaban hukumar NCC Farfesa Danbatta ya yi alkawarin taimaka wa Hukumar INEC samun nasarar zaben shekara 2019 ba tare da magudi ba.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.