Kiwon Lafiya Da Wutan Lantarki: Kasar Koriya Ta Arewa Za Ta Kai Dauki A Neja

93

- Advertisement -

Tsare-tsare sun yi nisa na hadin guiwa tsakanin gwamnatin Neja da kasar Koriya ta Arewa, kan samar da ingantaccen tsari kan kiwon lafiya, samar da abubuwan more rayuwa da ingantaccen wutan lantarki.

An cima matsayar ne a minna, bayan ziyarar da jakadan kasar Koriyar ta Arewa a Najeriya, Mista Jong Yong Chol, ya kawo wa gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Sani Bello. Ya ce gwamnatin jiha za ta inganta wannan zumuncin ta yadda za ta iya cin moriya wani abu daga kasar Koriyar ta Arewa.

Ya bayyana cewar gwamnatinsa na kokarin ganin ta samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya, wanda yake muradin ta zama na daya a bangaren kiwon lafiya ga ‘yan jihar da kasa baki daya, wanda zai rage kwararar masu zuwa ziyarar kasar Dubai kan kiwon lafiya, Indiya da Jamani, Kairo.

Gwamnan ya ce da wannan hadin guiwar da kasar Koriyan a bangaren kiwon lafiya, jihar za ta samu daukaka tattalin arziki saboda raguwar masu wajen dan neman lafiya. Ya cigaba da cewar jihar na da yalwataccen yanayi na samar da wutan lantarki ta hanyar anfani da madatsun ruwa ko na’urar tattara wuta mai anfani da hasken rana, wanda jihar za ta iya hadin guiwa da kasar don bunkasa wutan lantarki ga ‘yan jihar.

Gwamnan ya ce saboda gwamnati na bukatar samar da wutan lantarki ga al’ummar jiha, akwai shirin samar da wutan lantarki da bai wuce migawat 10-50 a karkashin tsarin (IPP) ga dukkanin kananan hukumomin jihar.

Ya gayyaci masu hari daga Koriyan da su mayar da hankali akan samar da karamar masana’anta kan tsarin IPP wanda zasu iya zuba jari a jihar, wanda ya tabbatar masu da su ci anfanin shirin na kafa masana’antar.

A na shi jawabin, ambasadan Mista Jong Yong Chol, ya baiwa gwamnan da al’ummar Neja tabbacin kasarsa za ta tabbatar ta hada hannu da gwamnatin jihar Neja dan ganin ta cimma burinta a wannan bangarora.

“ Maigirma Gwamna, ina cikin garin minna ne dan neman hanyar da zamu yi hadin guiwa da juna musamman a bangaren kiwon lafiya, ayyukan raya kasa da inganta wutan lantarki.

“ Kasarmu tana da abubuwa da dama da jihar nan ke bukata, wanda idan muka gabatar da su zai sanya jihar ta kara bunkasa da samun cigaba a bangarorin kula da kiwon lafiya, da cigaban kasa.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.