Kungiyar NLC Da TUC Sun Shiga Sasanta Rikicin Hukumar Kidaya Ta Kasa

96

- Advertisement -

Kungiyar kwadago ta NLC da na TUC sun shiga tsakani domin sasanta rikicin da taki ci ta ki cinye wa tsakanin Hukumar kidaya ta kasa (National Population Commission) da kungiyar ma’aikatan Hukumar.

Makwannin da suka wuce ne ma’aikata a humar suka shiga yajin aiki domin nuna rashin amincewarsu da sake nadin Dakta Ghaji Bello a matsayin shugaban hukumar, su na zarginsa da rashin iya aiki da mulkin kama karya da kuma kawo cikas a shirin da ake yin a kidayar alummar kasar nan na “Enumeration Area Demarcation EAD”

Sun ce, nada shi ya kauce wa tsarin wannan gwamnatin na yaki da cin hanci da tsarin tona asirin almundahana da ke gudana a ma’aikatu na “whistle blowing”

Da ya ke jawabi a ofishin hukumar ranar Litinin, shugaban kungiyar kwadago ta kasa Mista Ayuba Wabba ya ce, sun yi taro da hukumomin da suka kamata a kan rikicin, “Yanzu mun samu cikakken bayanin yadda rikicin ya ke, a da muna tunanin ma’aikatan na nuna rashin amincewarsu ne a kan nadin da shugaban kasa ya yi ne”

Ya ce, duk da cewa, ma’ikata na da gaskiya amma yadda suka tunkari lamarin ne ke da matsala, saboda haka zamu yi taro a ofishin sakataren gwamnatin tarayya ranar Talata domin tattauna yadda zamu magance matsalar.

Ya kuma bukaci a tattara bayanai da shaidun zarge-zargen da ake yi wa shugaban Hukumar domin gabatar wa a taron da za a yi.

“Zamu yi taro da sakataren gwamnatin tarayya, lallai kuna da gasikiya a wannan rikicin amma yadda ku ka bagatar da lamarin ne ke da matsala, abin da muke bukata yanzu shi ne a tattara bayanai da hujjoji domin gabatar wa a wajen taron”

Daga nan ya bukaci ma’aikatan su koma bakin aikinsu ya kuma tabbatar musu da cewa lallai za a maganin matsalolin da ke fuskantar su.

A nasa bayanin shugaban TUC Mista Bobboi Kaigama, ya ce, za a fuskanci matsalar ba tare da jingina siyasa ko kabilanci ba.

“Muna tabbatar muku da cewa, za mu yi magani wannan matsalar ba tare da tsoro ba, abin da muke bukata shi ne a kawo mana hujjojin da zamu yi amfani da su gobe a wajen taron, mu ‘yan kasa masu bin doka da oda ne, za kuma mu yi amfani da wannan daman domin biyan bukatunmu kamar yadda doka ta tanada, saboda haka muna bukatar goyon bayan ku” in ji shi.

Da ya ke karin haske a kan rikicin, daya daga cikin shugabannin kungiyar ma’aikatan Hukumar Kidayar Mista Hussein Ishiaku ya ce, ba wai suna kalubalantar nadin da shugaba Buhari ya yi na Dakta Bello ba ne amma suna bayyana cewa ne, wa’adinsa na farko na tattare ne da tambayoyi da yawa na rashin iya aiki da rashin gaskiya.

“Mun bayyana musu cewa, ba wai muna kalubalantar nadin da shugaba Buhari ya yi wa Dakta Ghaji Bello ba ne, amma halayyar da ya nuna ne a wa’adinsa na farko muka ga ya sha ban-ban da tsarin wannan mulki na Shugaba Buhari” in ji shi.

Ya ce, duk da ma’aikata sun nuna mamaki a kan yadda jami’an tsaro suka nemi shigar da sabon shugaban hukumar ofis da karfin tsiya amma shigowar kungiyar NLC da TUC ya taimaka maganin matsalar.

“Da muka shigo da safen nan mun yi tsammanin zamu ga karin ‘yansanda, amma daga dukkan alamu gwamnati ta canza shiri, watakila saboda sun ga kungiyar NLC da na TUC sun shigo don shiga tsakani, amma lallai tattaunawarmu dasu ya amfanar kwarai da gaske.

“Abin nufi a nan shi ne daga gobe kungiyar NLC da TUC ne zasu ci gaba gwagwarmaya a maimakonmu da gwamnati, matsayarmu dai shi ne ko zamu koma bakin aiki to ba tare da Bello a matsayin shugaba ba” in ji shi.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.