Mata 500 Ne Suka Samu Horo Kan Sana’o’in Dogaro Da Kai Daban-Daban A Dass

90

- Advertisement -

Wata kungiya mai zaman kanta wato kungiyar ‘ci gaban Matasan Hausa da Fulani’ ta samu nasarar horar da mata dari biyar 500 kan sana’o’in dogaro da kawukansu a fannonin sana’o’i daban-daban a karamar hukumar Dass da ke jihar Bauchi.

Shugaban kungiyar Musa Muhamamd shi ne ya bayyana hakan a lokacin bikin yaye daliban da suka samu horon a garin da Dass.

Alhaji Musa Muhammad ya ce, wadanda suke cin gajiyar shirin an basu horon ne a kan sana’o’in dogaro da kai daban-daban da suka hada da bangaren hada sabulu, jakurkuna da kayyan kamshin daki hade kuma da sinadaran gyaran gashi da sauran sana’o’in hanu.

Ya ce, horoswar wani bangare ne na yunkurin kungiyar wajen tallafa wa gwamnati na kokarinta na yakar zaman kashe wando da rashin aikin yi da ya yi katutu wa wasu jama’an jihar baki daya.

Ta bakinsa “Kuma dukkanin wadannan abubuwan da ka gansu mai girma gwamna daliban da suka samu horon nan sune suka hada su da hanyayensu da kuma horon da suka samu daga garemu. Sun iya sarrafa wadannan abubuwan ne a cikin wata guda da muka ware ana koyar da su sana’o’I wadda, su ka zo suka yi wadannan da hannayensu don haka da bukatar a dafa musu domin su ci gaba da tallafa wa kawukansu”. A Cewarsa.

A nasa bangaren, Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya ce gwamnatinsa a shirye take ta fuskacin hada hadu wa kowace irin kungiya dake da zimmar tallafa wa mata da matasa don basu damar dogaro da kawunakansu kansancewarsu masu amfani wajen ci gaban al’umma.

Gwamnan wadda ya samu wakilci, shugaban hukumar samar da aiyukan yi wa mata da matasa a jihar Bauchi Barista Faruk Gwadabe ya bukaci kungiyar da ta baiwa gwamnatin jihar sunayen wadanda suka samu horon domin nazarin yadda gwamnatin za ta taimaka musu da tallafin ababen da za su samu domin ci gaba da riritawa a gidajensu domin cimma burin da aka sanya a gaba “muna bukatar wannan kungiyar, su shuwagabanninta da su tura mana da sunayen mutane dari biyar da suka ji gajiyar wannan horon domin samun tallafi daga gwamnatin jihar Bauchi”, a cewarsa.

A nasa jawabin, shugaban shiyyar Arewa Maso Gabas na gidan rediyon Tarayya Malam Yahaya Abdullahi Mai Kano ya yaba da kokarin kungiyar ne wajen tallafa wa mutane domin dogaro da kawukansu.

Daraktan wadda ya samu wakilcin shugaban gidan rediyon Tarayya da ke Bauchi wato Globe Fm, Malam Abdullahi Gombi ya bayar da tabbacin hadin kai wa kungiyar domin cimma manufofinta na tallafa wa jama’a, sai ya bukaci sauran kungiyoyi da su yi koyi da hakan.

Shi ma a jawabinsa an fatan alkairi, mai Martaba Sarkin Dass, Alhaji Usman Bilyaminu Usman ya shawarci masu ci gajiyar shirin da su tabbatar da tallafa wa nakasa da su domin fadade hanyoyin koyon sana’a “ke da kika koyi sana’ar nan ki yi kokarin jawo kannuwarki, ko ‘yarki ki koya mata”.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.