NDLEA Ta Damke Mutum Hudu A Adamawa

85

- Advertisement -

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a jihar Adamawa, ta cika hannu da wasu mutum hudu dillalan miyagun maza biyu mata biyu a Yola fadar jihar Adamawa.

Da yake gabatar da mutanen ga manema labaru a ofishin hukumar da ke Yola shugaban hukumar Mista Yakubu Kibo, ya ce a farkon shiga wannan sabuwar shekarar ne, hukumar ta kame mutanen hudu bisa zargin shigo da miyagun kwayoyi jihar.

Ya ce hukumar na zargin mutanen da hannu wajan shigo da wasu haram tattun kayayyakin mayen da suka kai kilogiram 708.2, hadi da kimanin kilogiram 25.6 na tabar wiwi ‘yar waje da mutanen sukayi safararsu.

“wannan irin tabar wiwi (Cannabis Skunk) ta daban ce, da itace ta farko da’aka taba shigo da ita Yola fadar jiha da yawa haka, ana siyar da kowace daurinta kan naira dubu goma sha biyar (15, 000).

“taba ce mai matukar illata rayuwar mai shanta da maishe mahaukaci dan take, saboda Ita ta dinka wiwin da’aka sani sau uku zuwa sau hudu karfi, tana da saurin haukata mai shanta.

“kwararron ma’aikatan mu suka ganota a cikin wata motar Ludurious Bus da ta taho daga Lagos, mun ci gaba da bincike muka kame mutum mutum uku da hannu wajan shigo da ita” inji Kibo.

Shugaban hukumar ya kuma koka da karuwar shigo da miyagun kwayoyi a jihar, da cewa “daga wajan Janairun 2017 zuwa yanzu hukumar ta kame motoci 10 da suke dauke da miyagun kwayoyi, wanda kuma kotu ta mallaka motocin ga gwamnatin tarayya”.

Mista Yakubu Kibo, ya nuna damuwa bisa yadda mata ke kara shiga harkar dillancin miyagun kwayoyi a jihar, ya ce yanzu haka akwai mata biyu da suke tsare dasu bisa zargin shigo da miyagun kwayoyin jihar.

Ya ce, “wannan bakin ciki ina kira ga iyaye da su maida hankali su kuma rika kusantar ya’yansu domin sanin halin da suke ciki, hakan zai taimaka wajan kada kotu ta tura yaran gidan kasu” Kibo ya jaddada.

Shugaban hukumar yayi amfani da wannan damar wajan shawartar jama’a kira da cewa bai kamata su bari ana dakwan miyagun kwayoyi da motocinsu ba, ya ce domin duk motar da suka kame sun yi asararta, saboda kotu ta mallawa gwamnatin tarayya.

Daga nan sai kuma ya koka game da matsalar rashin kayan aiki musamman na zamani, ya roki gwamnatin tarayya da ta samar musu da kayan aiki domin aikin ya tafi da zamani.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.