Sarakuna Sun Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Karshen Kashe-kashe A Nijeriya

89

- Advertisement -

Kungiyar sarakunan gargajiya na Nijeriya (NCTRN) ta bukaci gwamnati Nijeriya da ta kawo karshen kashe-kashen da ake yi a sassan kasar nan, suna mai cewa, rayuwa na da mahimmanci bai kamata a rinka barnatar da rayukar mutane haka kawai ba.

Shugaban kungiyar ta NCTRN kuma Sarkin Musulmi Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammad Abubakar, ya yi wannan kiran a jawabinsa na bude taron kungiyar sarakunan gargajiya na kasar nan da ya gudana a Fatakwal ta jihar Ribas ranar Talata, ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti na musamman da zasu binciki dukkan kashe-kashen da aka yi a sassan kasar nan.

Leaershp A Yau ta gano cewa, taron wannan shekarar na da taken “Community Policing as a catalyst to Crime Prebention: The Role of Traditional Rulers.” ya kuma nemi gwamnatin tarayya da jami’an tsaro su kara kaimi wajen fuskantar aikinsu na kare rayuwa da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.

“A wannan taron namu zamu tattauna matsalar in har laifin daga gwamnatin tarayya yake zamu nemo hanyar warware wa tare da ba gwamnatin tarayya da alumman kasar nan shawarwarin hanyar da za a bi domin samu dawamanman zaman lafiya a kasar” in ji shi.

Ya ce, Sarakunan gargajiya na da ‘yancin bayyanawa matsayin alamari yanda yake ba tare da wani tsoro ba domin samun yadda kasarmu zata ci gaba.

“Tsarin mulki da sarautar gargajiya na nan tun kafin shekarar da turawa suka hada kasar nan a shekarar 1914, ba kaman ofishin siyasa bane da suke tafiya lokaci zuwa lokaci kuma suna da wa’adi, ya kamata mu hada kai a matsayinmu na sarakunan gargajiya domin gina Nijeriya”

“Ya kamata mu gina ‘yanuwantakar dake tsakaninmu har zuwa kan talakawanmu, mu kuma tabbatar da muna aiwatar da abin da muke fadi”

“Wannan haduwa namu nada matukar mahimmanci, haka na nufin babu abin da zai iya raba mu, saboda haka ya kamata mu yi amfani da mutuncinmu wajen rage tarnakin dake cikin kasa, lallai wannan lokaci ne dattawa zasu yi wa Nijeriya aiki, dole mu yi tsayin daka mu fuskanci masu son rusa kasar nan” in ji shi.

Daga nan Sultan ya lura da cewa, kasancewar Nijeriya na cikin rukunin kasashen duniya baza a rasa masu son dagula kasar nan daga kasashen waje ba, ta hanyar amfani da addini da kabilanci, saboda haka ya bukaci jami’an tsaro su rinka neman taimako da hadin kan sarakunan gargajiya wajen warware matsalolin da zai iya tasowa.

A nasa jawabin, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ya yi kira na musamman ga sarakunan gargajiyan kasar nan da su kawar da harkar siyasa da kabilanci wajen fuskantar matsalolin dake fuskantar kasar nan a halin yanzu.

“Wasu bangaren kasar nan na gunagunin ana dannesu wasu kuma na bukatar a basu hakkokinsu, ya kamata mu hada kai wajen warware matsalolin kafin sauran jama’a su fara ganin laifinmu”

“Ya kamata mu ajiye siyasa a gefe daya, mu hadu da jama’ar da ke korafi mu yi kokarin yadda za a magance musu matsalolinsu ta hanyar gaya musu gaskiya”

“Nauyin yin wannan aikin ya an a kanmu ne, mu daina ganin laifin juna, mu fuskanci aiki kawai tare da barin surutu” in ji Ogunwusi.

Tun da farko Sarki Dandeson Jaja, Amayanabo of Opobo kuma shugaban kwamitin shiye-shiryen bukin, ya ce ‘yan Nijeriya sun kosa su ga abin da zai fito daga bangaren sarakunan gargajiya.

Jaja ya bukaci gwamnatin tarayya da sarakunan gargajiya su a jiye harkar kabilanci da wasu banbance-banbance “Mu fuskanci yadda zamu warware matsalolin kasar nan”.

“Ya kamata gwamnatin tarayya su magance matsanancin tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan tare da magance rikicin rashin tsaro a fadin tarayyar kasar nan” in ji Jaja.

Sugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar Ribas ya mika godiyarsa ga gwamnan jihar Riba bisa daukar nauyin taron sarakunan da ta yi, ya kuma bukaci sarakunan gargajiyar da su sake jiki su tattauna tare da fito da shawarwarin da zai amfani kasar nan.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.