Sharhin Fim Din ‘Hasashe’

96

- Advertisement -

Suna: Hasashe

Tsara labari: Abdullahi Amdaz, Bashir Dan Rimi.

Furodusa: Nazir Auwal Dan Hajiya

Director: Ali Gumzak

Kamfani: Ali Nuhu Team

Jarumai: Ali Nuhu, Garzali Miko, Hafsat Idris Barauniya, Sadiya Adam, Bilkisu Abdullahi, Ammar Umar, Hajara Usman da Amina Maiduguri.

A farkon fim din an nuna Najib (Garzali Miko) yana tare da budurwarsa Nabila (Sadiya Adam) tana yi masa korafin an saka musu rana amma har yanzu bai dai na kule kulen ‘yan mata ba, Najib ya ba ta hakuri akan cewar shi ba aurensu zai yi ba kawai karyace karacensa yake yi musu, a wani bangaren kuma aka nuna shi Najib da budurwarsa a wurin shakatawa yana ta yi mata karya suna tare wata budurwar ta sake kiransa a waya akan cewar tana son ganinsa Najib ya ja gefe ya amsa wayar ya lallaba ta yace ga shi nan zuwa sannan ya dawo wurin wacce suke hirar ita ma ya sake yi mata karyar cewar babarsa ce ta kira shi, suka ciga ba da hirar a wurin shakatawar kwatsam sai ga wata budurwar ta kuma zuwa nemansa a gadin din ta kwalla masa kira ya yi wa wacce suke taren karyar cewar wacce ta kirawo shin ‘yar uwarsa ce ya ta fi ya je ya same ta ita ma ya shirya mata ta ta karyar ya taho ya barta kafin ya dawo wurin ita waccen ta farkon wata budurwar ta sa ta sake kwalla masa kira itama ya ya yi mata karya ya sallameta kafin dai ya bar wajen duk sai da ‘yan matan suka fahimta.

Sai gidan mujahid (Ali Nuhu) tare da matarsa Jawahir( Hafsat Idris) an nuna tana son ta yi aikin gwamnati saboda alkawarin da ya yi mata tun kafin su yi aure Mujahid ya je ya samo wa Jawahir aiki ya kawo mata ofa ta aiki Jawahir tana ta murna sai kuma kwatsam Mujahid ya lura cewar tana da karamin ciki a ta ke labari ya sha bam bam don sai ya hana ta aikin ya ce har sai ta haihu ran Jawahir ya baci sosai ta cigaba ta rainon cikinta har sai da ta haifi ‘yar ta Amira sannan ya amince mata ta fara aiki ya samar mata koyarwa amma sai dai kash idan ta fita wurin aikinta babu abinda ta ke yi sai sheke ayarta tare da Najib ba tare da sanin mijinta ba.

shi kuwa Najib ya auri Nabila amma babu abinda yake yi mata sai rashin arziki ga kuma kule kulen matan banza a waje har sai da takai ya yi wa wata budurwarsa ciki da ta je asibiti sai likita ya shaida mata cewar ashe ma tana dauke da cutar kanjamau wannan dalilin ne ya saka Nabila ta yi tafiyarta gidansu ta bar Najib ta shai da masa cewar ita baza ta iya zama da mai cutar kanjamau ba.

A gidan mujahid kuwa sakamakon rashin isashen lokaci na aikin gida da Jawahir ta ke yi saboda fita wurin aikinta ya sanya mahaifiyar Mujahid( Hajara Usman) ta samar masa ‘yar kawarta domin ta dinga ta ya su aikin gida kuma abin sai ya zama da arashi akan cewar wannan mai aikin budurwar Najib ce kuma sun hada baki da shi da ita domin ta dinga yi masa wasu bincike a gidan akan Mujahid Mai aiki tana zuwa ta shishshigewa Mujahid da kissa kala kala har sai da takai ya fara nemanta yakasance kullum Mujahid da Jawahir acikin shakku da rashin gaskiya suke akan ko dayansu ya gane abinda daya yake yi musamman tsoro akan ‘yarsu Amira ko zata tona wa junansu asiri tunda mai surutu ce domin ta taba ganin Najib tare da Jawahir sannan ta taba ganin Mujahid tare da mai aiki a dadi wannan ne ya janyo suke ta kaf kaf da Amira gudun kar ta tona musu asiri.

Abubuwan birgewa:

1-wakokin fim din sun yi dadi sun kayatar da masu kallo

2- Jaruman sun yi kokari wurin fito da labarin yanda mai kallo zai fahimta.

Kurakurai:

1- Shin wanene Najib? mai kallo kawai ya gan shi yana yaudarar ‘yan mata kuma daga bisa ni ya yi aure ko iyayensa ba’a taba nunowa ba ko anyi maganarsu ba.

2- Shin duk ‘yan matan da ya ke kulawa basu da gidan iyaye sai dai kullum a gansu a wurin shakatawa? sannan ya aka yi idan Najib yazo gurin shakatawa ‘yan matansa kullum ake arashi suke haduwa ko kuma sanar musu yake yi shi da ya ke abinsa a boye baya san asirinsa ya tonu?

3- Menene asalin sunan jarumin labarin acikin fim din (Garzali miko) masu kallo sunji wasu suna kiransa da Najib wasu kuma Kabir wasu kuma Abdurrashid har fim din ya kare ba’a tabbatar da tar tibin guda daya ba.

4- Akwai wurin da Najib yake chatting da burwarsa a gidansa kawai aka ga ya ajiye wayar ya ta shi matarsa kuma aka ganta ta zo ta dauka tana dubawa a wurin an nuna kamar don ta dauka ya ajiye ya ta, duk boye mata sirrikansa da yake.

5- An nuna Jawahir tana da karamin ciki a hotan gaba wanda aka kuma nuno su sai aka ga har ta haihu da aka kuma nuno su sai kuma aka ga har ‘yar ta girma dab da dab din ya yi yawa duk da fim ne ya kamata ace idan ma za’ayi haka to ace an rubuta bayan lokacin kaza.. sannan aga wani abin kuma ya faruwa.

6- Zaren labarin bai tafi ya dire ba sai ya dinga tafiyar hawainiya idan aka kunno matsala mai kallo ya karkatu akan ya ga ya abin zai karke sai kuma a sake kunna wata ba tare da an warware waccen ba har fim din ya kare abubuwa da yawa ba’a ga karshensu ba.

7- Camerar daukar hoto bata fita yadda ya kamata ba a fim din.

8- Bai kamata a ga mai aikin gidan mujahid ta ce masa wai bari ta shiga wanka ba shi kuma yace tohh a gaske hakan zai yi matukar wahalar faruwa menene alakarsu? tun da ba matarsa bace ina ruwansa da wankan ta.

9-Menene aikin da Najib ya fadawa budurwarsa zata yi masa a gidan Mujahid? tunda mai kallo bai ga wani abu da ta yi ba a zuwanta gidan na bincike ba kamar yanda Najib ya nuna.

10- A gaske zai yi matukar wahala budurwa ta yi wa saurayinta korafin yana kula kulan ‘yan mata sannan ya ce mata wai shi ba aurensu zai yi ba karya kawai yake yi musu kuma budurwar bata nuna wani bacin ranta ba, kawai ta yadda da abinda ya fadamata duk da an saka musu rana kamar yanda Najib ya fadawa Fadila.

Karkarewa:

Labari ne mai kyau amma bai sami tsari mai kyau ba shiyasa ya ruguje kuma an gaza wurin fito da ma’anar labarin sannan an gaza bai wa labarin karshe yanda ma mai kallo zai fahimci makasudin labarin. Allahu a’a lamu.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.