Wanda Ke Cikin Maye Zai Iya Aikata Kowace Irin Aika-Aika – Farfesa Khalifa Dikwa

92

- Advertisement -


Ba maganan a kama a daure ne kawai ba, ya wajaba gwamnati ta samar da ilimi ga yaranmu yanda ya dace, domin matukar yaro yana zuwa makaranta kuma gwamnati ta samar da dukkanin abin da ya dace na karatun nan, to za ka samu yaro ba shi ma da lokacin da zai zauna domin yin shaye-shayen nan.

Domin duk wanda ya kasance a cikin maye, to zai iya aikata kowace irin aika-aika ce. Don haka matsawar gwamnati da gaske take yi, to ya wajaba ta samarwa da yaranmu ingantaccen ilimi da kuma ayyukan yi. Muddin ba haka ba, Shugabanni suka ci gaba da kai yaransu waje da kuma manyan makarantu masu tsada suna karatu, sannan in sun gama su dawo suna yawo a cikin manyan motoci kamar gajimari, alhalin ‘ya’yan talakawa duk suna kallo, to su sani fa, “Ita rai, mai umurni ce da aikata ba daidai ba,” don haka komai na iya faruwa, Allah Ya sawwaka.

Farfesa Khalifa Dikwa, ne ya yi wadannan kalaman a wajen taron kaddamar da Kwamitin amintattu na Cibiyar gyara halayyar matasa da koya masu sana’o’i da ke Kaduna, wacce aka fi kira da Makarantar Malam Niga. An kuma yi taron ne a babban dakin taro na Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, a ranar Asabar 27 ga watan Janairu.

A nata jawabin, sananniyar Malamar nan, Dakta Y J Mibanyi, cewa ta yi, ba ta yadda za a tsarkake iyaye a kan aika-aikar da ‘Ya’yansu ke aikatawa, domin sau da yawa iyayen ne ke nu na halin ko’in kula ga kai-komon ‘ya’yan na su. Ya wajaba iyaye a kullum tun ‘ya’yayensu na kanana zuwa tasowarsu su san ina ‘ya’yayen na su suke, kuma da su wa suke zama ko tafiya yawo, su kuma san me suke aikatawa, yaushe suka bar gida, ina kuma suka je, yaushe suka dawo da makamantan hakan.

Shi ma Shugaban cibiyar wayar da kai ta kasa, Dakta Abubakar Omani, ya bukaci samar da wani zaunannen hadin gwiwa da cibiyar ta Malam Niga, domin fantsama sako da lungunan kasarnan a kan aikin wayar da kan.

Shi kuwa babban Daraktan nan na Cibiyar, ‘Alfa Care’ Honorabul Hasan Alfa, kira ya yi ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin Jihohi gåami da daukacin Majalisun kasarnan da su mike tsaye su tabbatar da samar da kakkarfar doka a kan masu safarar miyagun kwayoyi da abebadan da kan sa maye. A cewarsa, in har ba mai sayarwa, ba za a sami mai saye ba.

Shi ma tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, A D Ahmed, kira ya yi ga daukacin cibiyoyin duniya irin su UNESCO, da makamantansu, da su hada kai da wannan cibiya ta Malam Niga, domin tsarkace rayuwar matasa da al’umma baki daya. Sannan kuma ya yi kira da babbar murya ga gwamnatin Jihar Kaduna da ma sauran gwamnonin Jihohi, da kuma musamman gwamnatin Tarayya da su kawo wa wannan cibiya ta Malam Niga dauki a cikin gaggawa, domin a cewar shi, kaf a wannan kasar ba bu wata hukuma ko cibiya da ta tashi haikan wajen raba al’umma da munanan dabi’un da ba su dace ba kamar wannan cibiyar ta Malam Niga da ke Kaduna.

Babban Kwamanda Hukumar yaki da safara gami da tu’ammuli da muggan kwayoyi na Jihar Kaduna, N D L E A, wanda shima ya sami halarta gami da gabatar da jawabi a wajen taron, ya tabbatar da wancan kalamin na Shugaban Karamar Hukumar ta Kaduna ta Kudu, inda shi ma ya nu na, kaf a iya saninsa a wannan kasa tamu ba wanda ya san mahimmancin rayuwar matasa da kuma al’umma, ya kuma himmantu wajen raba al’umma da munanan halayen kamar Malam Niga.

Ya kuma nu na takaicinsa a kan yadda gwamnatoci suke wa wannan bala’in da ke rugurguza rayuwar al’umma rikon sakainar kashi. A cewarsa, bisa ga dukkanin alamu har yanzun gwamnatocin ba su shirya yakan wannan bala’in ba. Ya kuma bayar da misalin hukumar nashi, inda yake cewa, a wannan shekarar kwata-kwata Naira milyan 16 ne kacal aka ba su domin wai yakar safara da tu’ammuli da muggan kwayoyin, wanda hakan ya misalta da cewa, kila ko kudin man motocin na su ma ba zai isa ba.

Ya kuma kara da cewa, a kullum za ka ji ana ta batun shirya taruka a kan hakan, amma iyakacin maganar a wajen taron ne kadai, ba za ka ji an dauki wani kwakwaran mataki ba.

“A yanzun haka a dukkanin gidaje biyar na kasarnan, sai ka sami dan kwaya akalla guda daya, Ina ji mana tsoron nan gaba kadan, dukkanin Shugabanninmu a wannan kasar su zama ‘yan maye,” in ji kwamandan na NDLEA.

Kwamitin amintattun da aka zaba domin jagorantar cibiyar ta Malam Niga da ke Kaduna, sun hada da, Waziri Kanar Abdul mai ritaya, a matsayin Shugaban kwamitin na amintattu, sai Alhaji Dalhatu Ahmed, Dakta Y J Mibanyi, Dakta Muhammad Lawal Sabo, Farfesa Khalifa Dikwa, Dakta Maikudi, tsohon Shugaban Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Mubi.

Manyan mutane daga cikin kasarnan ne masu yawa suka halarci taron, daga cikinsu akwai, AC Metro Kaduna, Barista S A Balarabe, Kwamandan IMAN Task Force Kaduna, Sheikh Nasir, Kwamandan NDLEA Kaduna da dai sauransu.

Tun da farko, Shugaban Kwamitin amintattun, ya bayyana kadan daga cikin ayyukan cibiyar da suka hada da; Yaki da shaye-shaye, da kuma farfado da rayuwar mutanan da suka tsinci kawukansu a cikin wannan mummunar rayuwar ta shaye-shayen. Sannnan kuma cibiyar tana gudanar da ayyukan wayar da kai a makarantu tashoshin mota da sauran wuraren taruwar jama’a, a kan su nisanci mummunar dabi’ar ta shaye-shaye, su kuma rungumi zaman lafiya.

Cibiyar kuma tana agazawa marayu da masu karamin karfi, wadanda sune manyan gobe, ta hanyar koya masu sana’o’i. Tana kuma wayar da kan matasa maza da mata ta hanyar nu na masu alfanun zama lafiya, hakanan ba a bar cibiyar a baya ba, wajen yakar cutar nan mai karya garkuwar jiki ta, HIB/AIDS, a tsakankanin matasa, da sauran ayyuka makamantan hakan.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.