Yadda Masu Gadi Suka Kashe Wata Jami’ar Soja A Edo

92

- Advertisement -

Hankali ya tashi a layin Ugiagbe da ke garin Ugbor a karamar hukumar Oredo ta jihar Edo yayin da mai kula da lafitar wata jami’ar soja mai mukamin Manjo tare da wasu masu gadi suka kashe sannan suka kona gawar ta.

Majiyarmu ya muna cewa Manjo Ajuya na aiki ne a yankin Kudu maso Kudu ta dawo ne daga wani tafiya dai-dai karfe 9;30 na dare in da mai kula da lafiyar ta bahaushe ya tarbe ta daga baya kuma ya dirar mata da duka, daga baya wasu masu gadi su 8 suka hadu suka ci gaba da duka da saranta har ta mutu.

Majiyar tamu ta ci gaba bayyana mana cewa, bayan sun kashe ta ne sai suka watsa mata man fetur suka kuma banka wa gawar wuta, suka kuma sace kudade da kwanputan ta da gwalagwalan ta, bayan sun gama mugun aikin nasu ne suka sanar da jama’a cewa an samu hatsarin gobara ne ya kona shugaban masu har lahira, da jama’ar da suka taru ana kokarin kawar da gawar zuwa asibiti an lura masu gadin nata na kokarin kwashe abin da suka sata zuwa wani kangon gini. Daga baya ‘yansanda daga yankin Ugbor suka iso inda suka kama mai gadin ta tare da wadanda suka aikata kisan.

Wata mazauniyar unguwan da bata bukatar a ambaci sunan ta, ta ce “Wata mata ce ta sanar da ni cewa matar ta kone a kan gadon ta, mun shiga muka ga gawar a kasa, daga baya wasu makwabtan ta suka gaya mani cewa, masu gadin ta ne tare da hadin bakin wasu hausawa masu gadi suka kona ta bayan sun caccaka mata wuka”

“Sun kwashe kayayyakin ta da kudi har Naira 600,000 suka kuma kashe ta daga baya suka kona gidan gaba daya”

“Da farko mutane na tunanin sigari ne ya kawo gobaran amma da ake fito da gawan sai wani makwabcin ta ya lura da yadda gawar ya ke ya kuma lura da daya daga cikin masu gadin na kokarin wurga wasu kayayyakinta ta katanga, nan take ya sanar da jama’a aka bi shi aka kuma kame shi”

Lamarin ya tayar da hankalin mutanen unguwan, yayin da masu gadin da ke unguwan suka gudu bayan jin labarin mutuwar jami’ar sojan.

Da majiyar namu ya ziyarci gidan ranar Litini ya lura da wani bangare ya kone, gidan kuma na kulle, an dai fahinci cewa, marigayyar na zaune ne ita kadai yayin da yaran ta ke karatu a kasashen waje, wani makwabcin gidan ya nuna takaicinsa a kan yadda mai gadi zai kashe mai gidansa ba tare da wani hatsaniya tsakaninsu ba.

“Ba zamu yarda da masu gadi hausawa ba a wannan unguwan daga yanzu” in ji shi

Kwamishinan ‘yansanda jihar Mista Johnson Kokumo ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce tuni aka kama su, za a kuma gabatar da su gaban kotu da tuhumar kisan kai da zaran an kammala bincike. Sai dai ya ce, ba zai iya tabbatar da ko marigayyan Manjo ce a rundunar sojojin kasar nan.

Ya ce, dukkan alamu na nuna cewa, kisan kai ne, ‘Masu gadin sun kashe ta ne daga baya suka banka wa gidan wuta da nufin boye aika-aikan su. “Sai dai shugaban rundunar sojojin Nijeriya kadai ne zai iya tabbatar da cewa ko ita Manjo ce ko a a, amma a gare ni ita ‘yar Nijeriya ce kawai”

Kokarin jin ta bakin jami’in watsa labarai na Brigade ta 4 Kaptain Mohammed Maidawa ya ci tura don kuwa ya ki amsa waya bai kuma mayar da amsan sakon kar ta kwana da aka aika masa ba.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.