Yadda Na Kashe Mahaifina Don Yaki Daina…!!!

79

- Advertisement -

A Wani matashi Nuhu Bulus dan shekaru 17 a duniya da ke zaune a karamar hukumar Toro a cikin garin Bauchi ya kashe mahaifinsa mai suna Bulus Azi mai shekarun haihuwa 65 a duniya biyo bayan fizge abun da yake shan tabar wiwi da shi.

Lamarin ya auku ne a yankin Boloji da ke cikin Toro a ranar 17 ga watan Junairun nan na 2018 inda yaron ya kashe Babansa a bisa wannan dalilin na ya gan shi na shan sigari. Matashin wadda rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta baje wa manema labaru shi, da sauran masu laifuka daban-daban a ranar Alhamis din nan da ta gabata, matashin ya bayyana cewar babu wani takamaimai laifi wadda mahaifinsa ya yi ma ssa, ya kuma ce ba su da wata matsala a tsakaninsu amma dai kawai ya kashe shi ba tare da wani dalili ba.

Da yake amsa tambayoyoyin LEADERSHIP A YAU a lokacin da aka fito mana da masu laifin, matashin da ya kashe mahaifin nasa ya ce “Ni sunana Nuhu Bulus shekaru 17 a duniya. Abun da ya faru na zo nan shi ne a ranan ne dai muka samu matsala da ni da mahaifina sai na kwada masa Randa (abun anada ruwa) a tsakiyar kansa”. A ta bakinsa.

Ya ci gaba da yi mana bayani da cewa “Gaskiyar magana har ga Allah ni babu wani takamaimai abu da zan ce ga shi Babana ya min, abun dai da ya faru a ranar din ma ni dai kawai na bude idona ne na ganni a ofishin ‘yan sanda kawai”. A ta bakinsa.

Kana shaye-shaye ne? sai ya amsa da cewa “eh tabbas ni ina shaye-shaye, ina yawan shan kwayar Ikzon ne kawai”.

Ka ce mana ai kun samu matsala ne da mahifinka wacce matsace wannan? sai ya amsa da cewa “Sigari ne ya ke sha sai na fisge daga hanunsa. Amma ni ba a kan wannan sigarin ne na kashe shi ba, kawai dai ni na kashe shi ne”, a cewar Musa Bulus.

Ya kuma shaida da bakinsa cewar “Shi baban nawa na same sa ne yana shan sigari ‘LOFE’, amma ni babu wani abun da babana ya min”. Matashin yaron dai ya nuna kaduwarsa kan laifinsa da ya aikata inda ya yi nuni da cewar hakan na daga cikin sharrin shaye-shaye ne kawai, ya dai nanata ya kuma sake nanata wa manema labaru cewar shi fa mahaifinsa bai yi masa laifin asi ba.

Da yake yi mana bayanin yadda suka kama wannan yaron, Kakakin ‘yan sandan Jihar Bauchi DSP Kamal Datti Abubakar ya yi mana karin hasken yadda suka yi nasarar kamo yaron, ya ce, ‘ya’yan marigayin ne suka kawo rahoton aukuwar lamarin ga ‘yan sanda “A ranar 17/01/2018 wani mai suna Samaila Bulus da dan uwansa Musa Bulus dukkaninsu mazauna Boloji a karamar hukumar Toro, Bauchi suka kawo rahoto wa ofishinmu da ke Toro a kan cewar wani kaninsu mai suna Nuhu Bulus dan shekaru 17 ya kashe mahaifinsu mai suna Bulus Azi mai shekaru 65 a duniya”.

Da yake bayyana yadda yaron ya kashe mahaifisa ya ce, “Dan ya yi ta kwada wa mahaifinsa randa (Abun adana ruwa) babu iyaka wadda har ta kai ya ji masa munanan raunuka sosai”.

Ya ce, baya ga randan da yaron ya yi amfani da ita, ya kuma kwada wa mahaifinsa katakwaye babu iyaka.

DSP ya ce, nan take an hanzarta da marigayinn zuwa asibiti domin ceto rayuwarsa biyo bayan wannan farmakin da dansa ya kai masa amma hakai bai samu ba domin kuwa rai yayi halin sa, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa a babban asibiti da ke Toro.

DSP Datti ya ce daga cikin abubuwan da suka iya kamo yaron da su, sun hada da sassan randan da ya kwakkwada wa mahaifinsa da kuma kwatakwayen da ya yi amfani da su wajen dukan mahaifin nasa.

Sai ya yi bayanin cewar za su gurfanar da yaron a gaban kuliya domin fuskantar shari’a daidai da laifinsa na kisan kai.

Rundunar dai ta baje jerin masu laifukan ne da suka hada da masu garkuwa, ‘yan fashi, ‘yan damfara ‘yan sara-suka da dai sauransu.

Allah Ya Sauwaka

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.