’Yan Sanda Sun Kai Samame Wurin Tsafi A Binuwai Tare Da Kama Babban Boka

95

- Advertisement -

Rundunar sojojin Nijeriya sun kama wani boka da ake kira Tordue Gber (Tib Swem) wanda shiya ya ba ‘yan ta’addan nan ‘yan Akwazar Terwase (alias Gana) sa’ar arcewa shekarun baya.

Sanarwar da ta fito daga bakin jami’in watsa labarai na rundunar sojojin Nijeriya Sani Usman, ya ce a ranar Talata ne jami’an rundunar suka kama bokan a garin Tor-Dunga da ke karamar Hukumar Katsina-Ala a yayin da suka kai samame da sanyin safiya.

Mista Usman, ya ce, jami’ai ne daga runduna na musamman na “707 Special Forces Brigade” suka yi aikin kama Mista Gber.

Idan za a iya tuna wa tun shekarar 2016 jami’an tsaro ke neman Terwase ruwa a jallo.

“Binciken farko ya nuna cewa, wajen tsafin na Tordue Gber (Tib Swem) ya zama wajen bauta da maboya ga ‘yan ta’adda da kuma wajen bayar da shawari da yadda zasu tsara harin ta’addancin da suke kai wa jihohin Biniwai da Nasarawa da kuma Taraba.

“An kama bokan ne tare wani abokin harkarsa mai suna Kuwe Francis yayin da suke shirya kai hari da kuma yin garkuwa da Mista Zaya na kauyen Tse Bente da ke karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar Binuwai” in ji shi.

Usman ya kara bayar da hasken cewa, jami’an sojojin sun bindige Mista Tordue yayin da ya yi gardama lokacin da ake kokarin kwace makamin da ke hannunsa. An kuma kama bindigogi kirar gida guda biyu da albarusai guda 11 da mashina guda 3 tare wasu layu a wajen matsafan da kai samamen, sauran abubuwan da aka samu a maboyar tasu sun hada da wayan tafi da gidanka guda 2 da kuma janareta guda 3.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.