Yan Wasan Arsenal Sun Ji Kunya, In Ji Wenger

81

- Advertisement -

Kungiyar kwallon kafa ta Swansea City ta ci kungiyar kwallon kafa ta Arsenal 3-1 a gasar firimiya wasan mako na 25 da suka kara a ranar Talata.

Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hannun Nacho Monreal, dan kasar sipaniya a daidai minti na 33 da fara wasan, sai dai kuma minti daya tsakani Swansea ta farke ta hannun dan wasanta Sam Clucas.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Swansea ta kara na biyu ta hannun Jordan Ayew kuma daf da za a tashi daga karawar Sam Clucas ya ci kwallonsa ta biyu kuma ta uku ga Swansea.

Da wannan sakamakon Swansea wadda ta yi wasa 25 ta koma ta 19 da maki 20, yayin da West Brom wadda ta yi wasa 24 ta koma ta 20 da maki 20.

West Ham United da Crystal Palace tashi suka yi kunnen doki 1-1 yayinda Liberpool ta lallasa Huddersfield daci 3-0

Mai koyar da yan wasan kungiyar Arsenal, Arsene Wenger, ya bayyana cewa yan wasan kungiyar sun ji kunya saboda bai kamata suyi rashin nasara ba a hannun Swansea kuma ya kara da cewa dole sai sun sake kula sosai domin wasanni suna tafiya

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.