Za A Yi Musanye Tsakanin David Luiz Da Giroud

118

- Advertisement -

Rahotanni daga kasar ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta shirya bayar da dan wasanta, David Luiz ga kungiyar kwallon kafa ta Arsenal domin ta karbi Olibier Giroud, dan wasan gaba, wanda shima yake shirin barin Arsenal din.

Chelsea dai tana neman dan wasan gaba wanda zai cigaba da taimakawa dan wasa Albaro Morata wanda kungiyar ta siyo daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid sakamakon dan wasan yana yawan tafiya ciwo.

Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tace bazata siyar da dan wasan ba sai har idan tasamu wanda zai maye mata gurbinsa inda ake tunanin kungiyar tana gab da kammala cinikin dan wasa Aubameyang daga kungiyar kwallon kafa ta Dortmund.

Kungiyar Chelsea dai a shirye take data rabu da dan wasa Luiz bayan sun samu matsala tsakaninsa da mai koyar da yan wasan kungiyar, Antonio Conte, sannan kuma yanzu kungiyar tasamu wanda ya maye mata gurbinsa wato Christensen har ila yau kuma tana gab da kammala cinikin dan wasan baya, Palmeri daga kungiyar kwallon kafa ta Roma dake kasar italiya.

Tun da farko dai Chelsea tafison daukar Giroud a matsayin aro domin Arsenal tayiwa dan wasan kudi fam miliyan 35 wanda Chelsea take ganin yayi tsada duba da irin shekarunsa sai dai zatayi amfani da David Luiz domin samun sauki wajen daukar giroud din.

Arsenal dai tanason dan wasan baya domin kara karfin yan wasan bayanta bayan da tun farko ta nemi dan wasa Jonny Evans daga Westbrom sai dai yayi tsada kuma yanzu tana ganin zata dauki David Luis wanda zaifi saukin samu.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.