Jamiyar APC Ta Shirya Wa Zaben Kananan Hukumomin Kano

92

- Advertisement -

An bayyana cewa jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Birnin Kano, wacce dama can tana da karfi na samun nasara saboda goyon baya da hadin kai da fahimta da al’ummar yankin take da shi ga jagororinta suna da kishin al’umma da son su ga sun kawo abubuwan da za su ciyar da su gaba. Jagoran Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Birnin Kano, Tsohon Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Muktari Ishak Yakasai ne ya bayyana hakan.

Ya ce duk mutanen da suke mu’amala da su a matakai daban-daban, tun daga akwati da Mazabu har zuwa matakin Karamar Hukuma suna zaune da mutane lafiya, duk inda suka karkata a harkar siyasa, wanda shi ya sa ake ba su hadin kai da goyon baya, ake biyosu a tafi tare don cimma nasara.

Jagoran APC a Birnin Kano da kewaye ya ce tun daga wajen fitar da ‘yan takara, zabe suka yi, duk wanda yake da bukata ya tsaya takara ba wanda aka hana, a haka aka fitar da ‘yan takarar Kansiloli da na Shugaban Karamar Hukuma da Mataimakinsa, duk kuma abin da ake yi, sai an tara duk wanda yake da hakki sun gaya masa ga umurnin da uwar jam’iyya da ta jiha ta bayar, su kuma a matsayinsu na jagorori sun isar da shi zuwa kasa. Da wannan tsari Allah ya ba su nasara suka fitar da Alhaji Sabo Dantata a matsayin dan takarar Shugaban Karamar Hukumar Birni na APC da Mataimakinsa, Dan Bello Aminu.

Alhaji Muktar Ishak yace sun kamanta adalci anbi mazaba mazaba a wajen gudanarda zaben na fidda gwani ba wanda aka tursasa ko akayi masa tilas ga akace ga wanda zai zaba,aka hadu akayi zabe aka zabi Alhaji Sabo Dantata dan mutumne mai kishi wanda ya bada gudummuwa a shugabancin karamar hukumar da yayi na baya” wanda zuwana nima da nazama shugaban karamar hukumar Birnin kano da kewaye muka dora akai wajen gina wannan yanki,wannan yasa mukaga gara a sake daukoshi ya dora akan abinda ya fara dan cigaban al’ummar yankin”.

Alhaji Muktar Ishak Yakasai ya ci gaba da bayyana cewa a yanzu haka suna kokarin yin maslaha da duk wadanda suka shiga zaben fidda gwani da, ba su kai ga nasara ba, wanda yake ganin ba a yi masa daidai a matsayinsu na ‘yan jam’iyya daya suna lallashinsu don a hada kai a sami nasara gaba daya.

Yanzu haka a mazabun yankin 13 suna tarurruka na jam’iyya da fadakar da mutane kan tsare-tsaren da za a zo da su don kaiwa ga samun nasara da ci gaban al’ummar yankin.

Alhaji Dokta Muktar Ishak Yakasai ya yi kira ga al’ummar Karamar Hukumar Birni su zama masu bin doka da oda su tsaya su kare mutuncin abin da suka yarda da shi, ranar zaben Kananan Hukumomi da aka sa ran 10 ga watan biyu su fito su baiwa Alhaji Sabo Dantata da Mataimakinsa da Kansiloli 13 goyon baya, domin wannan kunshi na Shugabanci da za a samu suna fata za su aiwatar da ayyuka na ci gaban sama da abin da su suka aiwatar a baya ba don su sun gaza ba, sai don kara bunkasa ci gaban Karamar Hukumar Birni da kewaye.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.