Obasanjo Ya Furta Dalilin Da Yasa Ya Soki Mulkin Buhari

82

- Advertisement -

A Yau Ya sanar da haka ga manema labarai a garin Abeokuta bayan kaddamar da sabuwar kungiyarsa mai rajin ceto Nijeriya daga halin da take ciki

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana dalilin da ya sanya ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a wasikar da ya fitar kwanan baya.

Game da wasikar wanda Obasanjo ya shawarci shugaba Buhari da ya jingine batun zarcewa a karagar mulki, tsohon shugaban kasa yace yayi hakan ne don amfanin shi Buhari da ma yan kasa baki daya.

Ya sanar da haka ga manema labarai a garin Abeokuta bayan kaddamar da sabuwar kungiyarsa mai rajin ceto Nijeriya daga halin da take ciki mai take “Movement for the coalition of Nigeria” jihar Ogun.

A bikin kaddamar da kungiyar sa wanda ya samu halartar tsohon gwamnan jihar cross rivers

Donald Duke da tsohon gwamnan jihar Osun

Olagunsoye Oyinlola , Cif Obasanjo ya bayyana cewa ya gaisa da shugaban kasa a taron majalisar kasashen Afrika  a garin Addis Ababa bisa tarbiyan da yake dashi irin na al’adar yarbawa kuma yayi hakan ne ba tare da da la’akari da wasikar da ya tura ma shugaban ba.

Shi dai tsohon shugaban kasa yace shi dai ya bayyana ra’ayin sa ne game da gwamnati ba don wata manufa ba illa kishin kasa da yake da ita a zuciyar shi.

Game da sabon kungirya sa wanda aka yi ma rejista, Obasanjo ya dau alkawarin barin ta idan har ta samu karbuwa ta zama jam’iyar siyasa.

2019 Akwai Rikici Fatanmu Allah Ya Yanuba Mana Lokaci Yakuma Sanya Lokacin Babu Halakar Da Juna.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.