Da Alamun Isco Zai Bar Real Madrid

101

- Advertisement -

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafata Manchester City ta fara zawarcin dan wasan gaba na kwallon kafa ta Real Madrid, Isco domin siyan dan wasan idan kakar wasa ta kare.

Dan wasan dai yana cigaban da samun matsalar lokacin buga wasanni akai-akai sakamakon mai koyar da yan wasan kungiyar yafi amfani da yan wasan kungiyar na gaba wadanda sukafi shahara wato Bale da Ronaldo da Benzema.

Hakanne yasa dan wasan yafara tunanin barin kungiyar domin samun kungiyar da zata bashi wasanni da yawa inda tuni Manchester City daman ta taba neman dan wasan a kakar wasan data gabata ta sake komawa

Mai koyar da yan wasan kungiyar Manchester City, Pep Guardiola, yana son siyan dan wasanne domin ya maye gurbin dan wasa Dabid Silba, wanda shima dan kasar Sipaniya ne kuma ya shafe kusan shekaru 8 a kungiyar ta Manchester City.

Har ila yau wasu rahotanni sun bayyana cewa Manchester City ta shirya bayar da dan wasanta, Barnado Silba ga kungiyar Real Madrid domin ta karbi Isco sannan ta cikawa Madrid din kudin da zata bukata.

Ana tunanin kungiyar Real Madrid zata rabu da dan wasan sakamakon shirin da kungiyar take dashi nayin garanbawul a kungiyar wanda ake tunanin har da Isco a yan wasan da ake tunanin zasu raba gari da kungiyar.

Isco dai kawo yanzu ya bugawa Real Madrid wasanni 221 sannan ya zura kwallaye 30 sannan kuma ya taimaka an zura kwallaye 51 tun daga lokacin da yakoma kungiyar daga kungiyar Malaga dake kasar ta Sipaniya.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.