Da Alamun Ronaldo Ba Yason Real Madrid Ta Siyo Neymar Ko Harry Kane

94

- Advertisement -

Kai Tsaye Rahotanni daga kasar sipaniya sun bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo, bayason kungiyar ta siyo manyan yan wasa kamar Neymar ko kuma Harry Kane na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham.

Rahoton kuma ya bayyana cewa siyo manyan yan wasa masu tsada a kungiyar zai ragewa dan wasan kima da daraja a idon shugabannin kungiyar da kuma yan wasa da magoya bayan kungiyar wanda hakan yasa baya son kungiyar ta siyo manya manyan yan kwallo.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta shirya yin garanbawul a kungiyar a kakar wasa mai zuwa inda kungiyar take saran zata siyo manyan yan wasan da suka hada da Neymar da Harry Kane da kuma Edin Hazard na kungiyar Chelsea.

An bayyana cewa Ronaldo baya bukatar kungiyar ta siyo yan wasan gaba musamman wanda tauraruwarsu take haskawa domin kada yasa a dena kallon Ronaldo din a matsayin wani gwarzo a kungiyar, matsayin da yadade yana rike dashi a kungiyar tun shekarar daya koma kungiuyar wato 2009.

Real Madrid dai tana cikin tsaka mai wuya a wannan kakar sakamakon bata fara buga wasannin wannan kakar da kafar dama ba inda a halin yanzu take mataki na hudu akan teburin na laliga maki 19 tsakaninta da wadda take mataki na daya wato Barcelona.

Ronaldo dai zai cika shekara 33 a ranar Litinin mai zuwa wanda hakan yake nufin kungiyar tana bukatar fara tunanin sake sababbin yan wasa kuma matasa a kungiyar domin ganin kungiyar takai matakin datake bukata na cigaba da zama babbar kungiya a duniya.

Dabid De Gea da Courtois suna daya daga cikin masu tsaron ragar da kungiyar take zawarci sannan kuma kungiyar tana son siyan dan wasan baya na AC. Millan, Leonardo Bannuci, dan kasar Italiya.

Kuyi Share Zuwa Ga ‘Yan uwa

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.