Dan Wasan Manchester City Mangala Ya Koma Everton

93

- Advertisement -

Everton ta dauki aron dan kwallon baya na Manchester City Eliakuim Mangala, dan kasar faransa har zuwa karshen kakar bana, inda zai fafata a gasar wasannin Firimiya.

Dan kasar Faransan mai shekara 26 shi ne na uku da kungiyar ta dauka a kasuwar siye da siyar da ‘yan wasa da aka bude ta watan Janairu, bayan Theo Walcott na Arsenal da kuma Cenk Tosun Basiktas ta kasar Turkiyya

Mangala ya koma Manchester City daga kungiyar kwallon kafa ta FC Porto dake kasar Portugal a shekarar 2014 akan fam miliyan 32, kuma wasa hudu kawai ya buga a gasar Firimiyar bana.

Ya bar kungiyar ne bayan da Manchester City ta dauki Aymeric Laporte daga Athletic Bilbao a kan fam miliyan 57.

Mangala ya yi wa Manchester City wasanni sau 79 tun bayan da ya koma kungiyar daga Portugal, sai dai ya kusan shafe kakar 2016-17 a kungiyar Balencia ta kasar Sipaniya yana buga wasa a matsayin aro.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.