FBI Da Fadar White House Na Ce-Ce-Ku-Ce

95

- Advertisement -

Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta diga ayar tambaya a kan kokarin da ake na fitar da wata wasikar sirri, wadda aka ce ta zarge ta da wuce gona da iri wajen amfani da ikonta na bibiyar abubuwa wajen matsa wa kwamitin yakin neman zaben Donald Trump.

“Muna matukar damuwa game da abubuwan da ba a saka a cikin wasikar ba da kuma yadda za su yi tasiri kan daidaton wasikar,” in ji hukumar FBI .

Ana rade-radin cewar za a iya wallafa wasikar sirrin ta majalisar dokokin kasar ranar Alhamis.

‘Yan Jam’iyyar Democrat suna fargabar cewar takardar ka iya kasancewa wani yunkuri na saka shakku kan sahihancin binciken alaka tsakanin kwamitin yakin neman zaben Trump da Rasha.

Dan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Democrat, Adam Schiff, ya yi zargin cewa takwarorinsa na jam’iyyar Republican sun sauya rubutun cikin takardar bayan an kada kuri’a a kanta.

Kuma ya ce, dole a janye takardar kuma a sake bibiyar ta kafin a fitar da ita bainar jama’a.

Lauya na musamman Robert Mueller shi yake jagonrantar binciken zargin cewa Rasha ta yi katsalandan da kuma yiwuwar cewa mukarraban Gwamnatin Trump sun aikata laifin hana aiwatar da doka.

Dole sai fadar White House ta amince a kafin a fitar da wasikar, amma Shugaban ma’aikatan fadar, John Kelly, ya shaida wa gidan rediyon Fod News cewa za a “hanzarta fitar da ita a nan” domin “duniya gabadaya” .

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.