Bazan Koma Real Madrid Ba Sai 2020 In Neymar

101

- Advertisement -

Rahotanni daga kasar sipaniya sun bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Neymar yayiwa kungiyar Real Madrid alkawarin cewa zai koma kungiyar a shekara ta 2020 idan dan wasan kungiyar, Cristiano Ronaldo tabar kungiyar.

Sai dai wani rahoton kuma yace shima Ronaldo din bayason zama a kungiyar ta Real Madrid indai Neymar din zai koma kungiyar saboda zai koma yana zama a bayan Neymar din.

Neymar ya bar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona zuwa kungiyar PSG ne a karshen watan Agustan daya gabata akan kudi fam miliyan 200 abinda yasa a yanzu yafi kowanne dan wasan kwallon kafa tsada a duniya.

Neymar dai yafara buga kakar wasan wannan shekarar da kafar dama inda a halin yanzu yazura kwallaye 17 cikin wasanni 20 daya buga a kungiyar wanda hakan yasa kungiyar a yanzu take kan gaba a gasar rukuni ta kasar faransa sannan kuma kuma kungiyar tafito daga cikin rukuni rukuni a gasar zakarun turai ta wannan shekarar.

Kungiyar PSG dai tanada yan wasan gaba da suka hada da Kylian Mbappe da Edinson Cabani a kungiyar ga kuma Neymar din wanda hakan yake nufin kungiyar tanada manyan yan wasan gaba kuma masu zura kwallaye a raga.

Dai dai an bayyana cewa Neymar bayason komawsa Real Madrid tare da Ronaldo wanda hakan yana nufin bazai koma kungiyar ba sai idan Ronaldo yabar kungiyar a nan gaba kadan.

A na tunanin nanda shekara biyu Ronaldo zai bar kungiyar ta Real Madrid sakamakon rashin jituwa dad an wasan yake samu da kungiyar musamman wasu daga cikin yan wasan kungiyar da kuma magoya bayan kungiyar a wasu lokutan.

Sannan har ila yau Neymar yanason yafi kowanne dan wasa samun albashi a duniya yanason yafi dan wasan Barcelona Leonel Messi da takwaransa na Argentina, Carlos Tebes.

A kwanakin baya dai mai koyar day an wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana cewa idan hard an wasan yanason komawa kungiyar suna maraba dashi kuma zasuyi kokarin ganin sun samu dan wasan .

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.