Sabuwar Jam’Iya Da Zata Kayar Da PDP Da APC ( Shiga Domin Ganin Wannan Jam’iya )

109

- Advertisement -

Jam’iyyar People Redemption Party (PRP) ta misalta jam’iyyar da ke mulkin Nijeriya a halin yanzu da cewar, jam’iyyar ce wacce ta yi mummunar mutuwa fiye da jam’iyyar PDP a lokaci da ta ke kan karagar mulki.

Da ya ke ganawa da manema labarai a Ilorin babban birnin jihar Kwara a ranar Asabar din nan, shugaban jam’iyyar ta PRP a jihar, Farfesa Mahmood Muhibeedeen Aliyu, ya bayyana cewar da APC da PDP dukkaninsu tunaninsu da kuma tsarin tafiyar da mulkinsu iri daya ne. Don haka ne ya bayyana cewa salo iri daya su ka shimfida a fadin Nijeriya.

Ya bayyana cewar, al’adar dukkanin gwamnati mai ci matukar ta biye wa tsarin da tsohowar gwamnati ta taho da shi tabbas ba za ta kai ga nasara a zaben gaba ba, domin a cewarsa Nijeriya na bukatar canji ne, ba wai biye wa tunani da kuma irin salon mulkin da APC da PDP su ka yi ba.

Shugaban jam’iyyar Aliyu ya bayyana cewar abun takaici ne a ce gwamnatin APC ba ta biyayya ga dokokin kotun kasa, inda ya bayar da misali da yadda gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu da umurnin kotu na sake tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, wato Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya) da kuma jagoran kungiyar ’yan uwa Musulmi ta Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, wadda kotunan su ka bayar da umurnin a sake su, amma gwamnatin APC ta yi biris, kamar yadda ya shaida.

Ya ce, da salon kin bin dokar gwamnatin PDP da na APC duk iri daya ne, ya na mai bayyana cewar ta ki ta fuskaci kawo cigaba ga kasa duk tsari daya gwamnatocin ke tafiya a kai bisa tunani wadda ba zai kai Nijeriya ga samun mafita ba.

Ya kara da cewa, “idan mulkin Nijeriya ya sake fadawa cikin wadannan sannanun jam’iyyun Nijeriya ta shiga ukunta. Najeriya na daf da fadawa cikin akwatin gawa matukar jam’iyya daya daga cikin APC ko PDP suka sake dalewa karagar mulki a zaben 2019.

“Domin dukkaninsu hadafinsu guda ne, tsarin gudanar da mulkinsu da tafiyar da gwamnatinsu duk iri daya ne, sannan uwa-uba ma dukkaninsu ‘ya’ya daya ne. ’Ya’yan uwa daya ne, kawai su na sauya sheka daga wannan jam’iyyar zuwa wancan jam’iyyar, don haka ne za ku ga abu guda ne ke wakanuwa a tsakanin gwamnatinsu a dukkanin fadin kasar nan. Kuma ku duba za ku ga hakan, tunani daya da kuma ra’ayi daya suke da shi.”

Shugaban ya cigaba da bayyana wa ’yan jarida cewa, “tun zuwan APC mulkin, cin hanci, rashawa da kuma yawaitar garkuwa da mutane gami da gurbawacewar abubuwa da dama sun ninku ne suka yi, a maimakon su raguwa”.

Ya ce, jam’iyya mai ci ta fadi warwas; “APC ta mutu ta lalace fiye da PDP. Ku lura da abun da ya faru a zaben gwamnan Edo; haka kuma labarin ya ke idan mu ka duba yadda zaben gwamna ya gudana a jihar Ondo. Haka idan mu ka dubi yadda zabukan kananan hukumomi su ka gudana a wasu sassan jahar.”

Ya ce, zai iya bugan kirji ya ce a dukkanin jam’iyyun da ake ganinsu APC da PDP babu wata jam’iyyar da za ta iya fidda Nijeriya daga halin ni-‘yasu illa jam’iiyar PRP, inda ya bayyana cewar sun san matsalar Nijeriya da kuma fitar da shimfidadden tsarin da zai kai Nijeriya tudun mun-tsira.

Sai ya bukaci dukkanin ‘yan Nijeriya da su mara wa jam’iyyar PRP baya domin ta samu zarafin shimdiya aiyukan alkairi domin kai Nijeriya mataki na gaba wadda APC da PDP su ka zaga yi.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.