Wai Kuwa Me Yasa Take Kuka Ne Haka….?

87

- Advertisement -

Wani mutumin da aka bayyana sunansa da Isaiah Zhou ya gamu da wata girgizar da ta kusa sanadiyyar raba shi da duniya a lokacin da ya shigo gidansa ya tarar da mai dakinsa kwance a kan gadonsu na aure tumbir ita da wani wanda ta dade da gabatar masa a matsayin kanin mahaifiyarta suna lalata

Isaiah Zhou wanda dan yankin Mberengwa ta kasar Zimbabwe ne ,ya yi yunkurin kashe kansa bayan da ya gano cewa ashe mutumin da matarsa, Elizabeth Ndlovu ta gabatar masa a matsayin kanin mahaifiyarta saurayinta ne tun suna makaranta

Rahotanni sun nuna cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata ne dai mista Isaiah ya shiga gidansa a lkacin da matarsa, Ndlovu bata tsammanin zai shigo, ko da ya bude kofar dakin barcinsu, sai ya sam mai dakin nasa da Aleck Moyo da ya ke dauka a matsayin kawun matarsa suna jin dadin junansu, inda nan take ya samu wani itace ya lakada musu dukan tsiya.

Kodayake dai bamu samu damar jin ta bakin Ndlovu da Moyo ba kafin wallafa wannan labarin, amma majiyar ‘yan sanda ta yankin Mberengwa tabbatar mana da cewa Isaiah ya dawo gida a kasa da lokacin da ya saba dawowa daga aiki sosai, inda ya tarar da mai dakinsa da wani wanda ta gabatar masa a matsayin dan uwanta suna lalata a cikin dakinsu kuma akan gadonsu na kwana

Majiyar ‘yan sandan ta ci gaba da cewa, ko kafin Isaiah ya kama matarsa da kwartonta sai da makwabata suka tsegunta masa cewa suna zargin matasa na soyayya da Aleck Moyo ne wanda ta gabatar masa a matsayin kanin mahaifiyarta, wanda hakan ne ma ya sanya zargi a zuciyarsa kuma ya dawo gida da tsakar rana daga wajen aikinsa da nufin ya kamasu.

Kuma ya yi sa’a ko da ya dawo sai ya tarar da gidan ba a kulle shi da mukulli ba wanda ya samu damar shiga gidan kai tsaye, ya kuma tarar da dakin nasu a rufe amma ba da mukulli ba shi ma.

Moyo da a halin yanzu ya tsere ba a san inda ya shiga ba, ya tsira da raunika daga dukan da Isaiaha wasu makwabta suka yi masa kuma ya gudu ba tare da shigar da karar keta masa haddi da aka yi ba wanda hakan ke nuna rashin gaskiyarsa.

Tuni dai Isaiah ya saki matarsa Ndlovu wacce dama ya tama samunta da laifin yin soyayya da wani mutum shekaru biyu da suka gabata, amma ta bashi hakuri ta ce ba zata kuma ba. Sai kuma yanzu gashi ya kara kamata tana zina da saurayinta a gidansa. Muna rokon Allah da ya bamu mata nagari.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.