‘yan Najeriya Zasuyi Wasan Barkwan ci Kan Yaki Da Cin Hanci

92

- Advertisement -

– An yi shi ne a harshen Hausa, za a kuma gabatar da shi ne a gidajen rediyo 8 a Arewacin Kasar na

– Wasan na da fitowa guda156 wanda za a fara gabatarwa daga makon farko na watan Fabrairu 2018 har zuwa 2020

Nan ba da dadewa ba za a fara gabatar da wasan kwaikwayo a kan yaki da cin hanci da rashawa a tashoshin rediyo 8 da ke Arewacin Najeriya. An yi wasan kwaikwayon ne da harshen Hausa a inda a ka kashe kudi naira miliyan 30 don shirya shi.

Ciyaman din Kwamitin Amintattu na Kungiyar ‘Yan Wasan Kwaikwayo na Najeriya (MOPPAN), mai suna Alhaji Abdulkarim Mohammed, shi ne ya tsarauma ya shirya wasan wanda a ka sa wa suna Shugabanci.

Mohammed ya bayyana cewar an shirya wasan ne don bayar da tallafi wurin yaki da rashawa a Kasar nan. Ma’aikatar Tallafi mai zaman kan ta, McArthur Foundation, ita ce ta dauki nauyin shirin.

Wasan ya na dauke ne da fitowa guda 156 wanda za a fara gabatarwa daga makon farko na watan Fabrairu na 2018 zuwa watan Fabrairu na 2020. Wasan kuma ya kunshi ‘yan wasa 22 ne wadanda a ka zabo su daga mutane 88 da su ka nemi fitowa.

Mohammed ya bayyana cewar wannan wasa shi ne irin sa na farko. An kuma yi amfani da na’urori gangariya wurin daukar sa. An kuma yi sa ne a waje, wurare daban daban da su ka danganci shirin ba a dakin daukan shirye-shirye ba.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.