Darakta Yakubu Muhammad Yace Bai Taba Son Waka ba

110

- Advertisement -

Tabbas, a duk lokacin da za a yi tarihin waka a masana’antar shirya fina-finan Hausa da ake wa lakai da ‘Kannywood’, Jarumi Yakubu Mohammed zai kasance a sahun gaba saboda irin tashe da jan zaren da ya yi a masana’antar na tsawon shekaru.

Tun daga kan dadin murya, salon sarrafa harshe, karangiya, amsa-amon-waka har zuwa kan kafiya d balaga, Yakubu ya baje kolin fasaharsa. Masoyaakokinsa daban-daban da Shafin Taurarin Nishadi ya taba jin ta bakinsu, sun bayyana ra’ayoyi mabanbanta kan abin da ya sa suke ‘mutuwar’ so wakokin Jarumin.

“Har yanzu ina jin wakokin Yakubu, za ka ji fasaha da fikira da basira a cikin irin kalmomin da yake zubawa a wakokinsa.

Wani lokaci idan Yakubu ya yi waka dole sai an koma wurinsa an tambaye shi wasu abubuwa da ya sanyo a cikin wakar saboda balagar harshe da Allah ya bashi. Sannan ga dadin murya, shi ya sa har gobe da safe ban iya sauraron wakokin fim fiye da na Yakubu”, in ji R. Indabawa.

“Gaskiya wakokinsa suna da dadi, suna sa nishadi, za ka ji idan kana jin ta ka tafi wata duniya mai ddi, kana yi kana gyada kai, ina kiran sa da ya cigaba da waka saboda a gaskiya ya iya”, in ji Suly Daurasko.

Wasu daga cikin fitattun wakokinsa sun hada da, Kantun Ghali, Jarumai, Adamsy, Kwalli, Attajirai, Jarida, Nagarta, Dandaralliyallilo, Dangaruwa, Sangandaliyo, E Ruwa Ye Ruwa, Jeren Kumbo, Tubali, ‘Yan Yara Ku Bar Zuki ta Malle da sauran su bila’adadin.

Sa dai kuma za a iya cewa, ga dukkan alamu masoya wakokin Yakubu za su ji banbara-kwai a ransu idan suka ji cewa Yakubun bai taba sha’awar waka a ransa ba duk da cewa ya yi fice a fagenta.

“Yau dai zan bayyana wani sirrin da ban taba fada wa kowa ba. Tun da nike ban taba son waka a zuciyata ba!”

Yakubu Mohammed ya cigaba da bayyana cewa “Na rasa yadda zan yi ne kawai amma tun farko ba na son yin waka har cikin zuciyata.” Mutane da dama za su yi mamakin yadda mutum zai yi abu har ya kai kololon matsayi a kai amma kuma ba shi da sha’awar abin a ransa, amma Yakubu ya nunar da cewa ba abin mamaki ba ne, inda ya bayyana asalin yadda aka yi ya tsinci kansa a cikin waka.

“Wata rana ina Iyantama (Kamfanin Iyantama Multi Media), sai ga wani zai yi fim yana so a yi masa waka; sai na ce ai kuwa zan rubuta masa waka. Bayan na rubuta yaron da zai rera sai ya kasa hawa wakar yadda ya kamata. Sai na fara rera masa don ya ji ya dauka.

Iyantama (Hamisu) sai ya ce to in rera wa yaron wakar mana idan ya je gida ya ji sai ya zo ya rera. Na rera wakar na gama, sai Iyantama ya ce wa mai fim din ga wakarka nan; kai kuma yaro ka yi hakuri. Ka ji yadda aka yi na tsinci kaina a waka”.

Toh ko yaya shararren mawakin ya ji a ransa a ranar da ya fara rera wakar alhali ba shi da sha’awar abin ko kadan a cikin ransa, ya ba da amsar cewa “A ranar da na fara waka bayan na gama sai da na kulle kaina a daki na yi ta rusa kuka, saboda banon abin a raina!” Yakubu Mohammed ya yi wadannan bayanan ne a tattaunawarsa da Jarumi Aminu Sharif (Momoh) a shirin Kannywood na Gidan Talabijin na Arewa 24 da ke Kano.
Tuni dai Yakubu ya yi nisa a halin yanzu a fagen fiowa a matsayin Jarumi a fina-finan Hausa daban-daban, da fina-finan da ake yi a kudanci da kuma wadanda ake shiryawa da harshen turanci a Ar

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.