Hanyoyin Da Zakibi Kisamu Miji

81

- Advertisement -

Maza su kan zama a rude yayin da su ka tashi neman mace tagari har su kan shiga shakka kan wace ce macen da ya dace su aura. Amsar da su ke samu ita ce, su yi duk inda za su yi su lalubi mai kamun kai, domin daga ita ne a ke samun mace tagari. Ita kuwa mai kamun kai siffofinta a bayyane ya ke, inda namiji in ka kura ido ka tsanannta nema, to za a dace.

Mace tagari ita macen da Bahaushe ke kira mai kamun kai wadda ta siffantu da kakkyawar dabi’a da halaye da kamala, wacce kuma kallo daya za a iya gane tarbiyyarta da kokarin da iyayenta su ka yi wajen ba ta tarbiyya. Mace ta kwarai ita ce wadda kowanne namiji mai hankali zai yi fatan a ce ta na gidansa ta zame masa sanyin idaniya ta zama al-mar’atissaliha da Annabi Muhammad (SAW) ya ce ta fi duniya da duk abin da ya ke cikinta. Mace ingantacciya ita ce dai matar da kowanne namiji zai so ya sami zuriya da ita.

Mata da dama da za ka tattauna da su shi ne babbar matsalarsu mijin aure, abin haushi da ke damun su ga masoyan nan kamar jamfa a Jos, amma auren ya gagara. Mata na ta wahala addu’a da ’yan dabaru kana su na ta fama, amma abu ya ki yi wuwa. Tashin hankalin ba ga matan ba zawarawan ba. Mace wadda ba ta da makusa ta kowanne bangare kyau ko asali ko ilimi, amma aure ya gagara a na ta laluben dalili an kasa gano gaskiya abu guda ke zagayawa a kwakwalwarsu shi ne maza mayaudara ne, amma fa duk yaudararsu su na neman mace tagari ne, don sa wa a daki.

Kamun kai

Idan ka tashi neman matar da za ka aura ka dage ka nemi mai kamun kai. Ya na cikin matakin farko da mace ya kamata ta fara nunawa a gun duk wanda ta ke so su kulla mu’amala da ta ke fatan dorewarta zuwa aure. Hanyoyi da dama za ka lura da shi in ka na son gane mace mai kamun kai, kada ka jira a ba ka labari; kai da kanka za ka sa ido ka lura. Mata a yau a tunaninsu yadda su ke ganin maza na haba-haba da mata ba tare da nuna wani zabe ba, to su sani iyakarta waje ne.

Sutura

Sutura ita ce abin da a ke sanyawa a jiki don kare tsiraici. A sutura a na gane kamalar mutum. Abu na farko da kan ja hankalin namiji ga mace har ya gane ajin da zai ajiye tashi ne irin suturar da ta saka jikinta.

Mata a yau su na tunanin bayyana tsiraicinsu shie hanyar da za su iya janyo hankalin namiji gare su har ya gane kyan wani bangare na jikinsu da zai kai su ga aure. Wannan kuskure ne, domin namjin da wannan zai dauki hankalinsa har ya yi tunanin ku yi sabo, to tabbas sai dai soyayya, wanda a karshe danasani ne zai biyo bayan haduwar. Ya na da kyau mace ta yarda da cewa mijinta duk inda ya ke zai tarar da ita, sannan ba wani dace da za a samu a sabon Allah.

Surutu

Surutu barkatai alamu ne na rashin kamun kai. Macen kwarai ba a san ta da daga harshe ba ko da a cikin ’yan’uwanta mata ne bare kuma maza. Wata matar ta na tunanin idan ta shiga dandazon maza ta daga muryarta da zakewa shi ne zai janyo hankalin namiji kansu. Mace mai surutu rau-rau a kan titi ko cikin maza ba ta cikin irin matar da ka ke nema ka aura.

Mace mai kamewa da karancin magana ko da kuwa a wajen saurayin ne abar yabo ce da soyuwa ko da batun auren ne irin su a ke nema a adana a gida.

Kunya

Bahaushe ya ce kunya marin da. Ka tabbatar matar da za ka aura mai kunya ce, don kuwa duk macen tagari an san ta da kunya da yakana da kara. Mace ba ta isa mace abin sha’awa idan har ta zamanto fitsararriya. Akwai hanyoyi da dama da mace za ta nuna kunya kamar haka:

Zance barkatai

Yin surutu rau-rau kafin namijin ya yi guda kin yi goma. In har aka zo batun aure maza ba irin wannan suke nema ba in har kina neman mijin aure to anan kin fadi jarrabawar. Ciye-ciye

Mata a yau sun zubar da kyakkawar al’adar nan ta kame kai wajen ciye-ciye a kan hanya ko gaban samari. Mace mai ciye-ciye da rashin kimtsi ko ga s’anninta mata ba ta farin jini bare maza. Duk mata da ka ganta tana ciye ciye kan turba bar ta kawai ba ta shirya samun mijin aure ba.

Roko

Roko shi ma wata hanya ce ta nuna rashin kunya da mata kan dauka hanya wayewa. Duk matar da ta fiye roko tana kashe wa kanta wata daraja ne ga mai sonta kuma in har mace ta fiye roko to fa tana nunawa wannan da zai aure ta irin zaman da za su yi. Hali na farko da za su sa a ran su in har suka kai ki gidansu ba za ki iya hakuri da samu da rashi ba sannan duk randa babu ba za ki iya rufa wa zamantakewar asiri ba. Roko ga mace babbar hanya ce ta zubar da mutunci. Don haka in budurwarka ta ishe ka da ba-ni-ba-ni na ba gaira ba dalili to fita a guje ba ba matar aure ce ba.

Kallo

A kallo kadai a na iya bayyana halin mace, tarbiyyarta da kunyarta da dacewa ka kai ta gida ko kuma ba za ka kai ta ba. Ka lura da yadda wadda za ka aura ta ke kafe ka da ido, ba rusanawa, to ka bi a sannu.

Rashin jan aji

Mace ta kirki da jan aji da kamewa a ka santa. Ba wai ta zama mai girman kai ba, amma ka nemi wanda ta san darajar kanta. Idan har mace za ta zama arha kowanne namiji ya kira ta ba tantancewa ta je, kowa yake bukatar jin hira ko yawo ita za a zo nema a tafi da an ce ana sonta to fa kasuwa ta bude ba sauran edcuse to fa mai irin wannan halin ta kade ba ta sa dan-ba ba a wajen neman mijin aure ba. Kai ma me neman matar kwarai kada ka leka.

Zafin soyayya

A nan ba sai na yi dogon sharhi ba ku maza ku ne ku ke lallabawa ku nemi yarinya da bukata ta biya ba kwa kuma komawa mu a bangarenmu mata sai mu ce rashin alkawari ne ya janyo haka amma ku kuka san dalili don haka ni a nan ba ni da ta cewa A wannan gabar ya ragewa matan tunda sai me karfin rabo saurayi ke neman mace a karshe ya aure ta. Na san zai yi wuya ko na ba ka shawarar idan haka ta afku duk da ba a fata nace ka aure ta ko na fad aba ji z aka yi ba.

Abin nufi dai da wannan rubutu shi ne kwarya tagari na rataya. Maza irin wannan suke nema su kai gida. Kalubale ne ga iyaye su sa ido kan tarbiyyar ‘ya’yansu sannan su ke nusar da su abubuwan da ya dace na tarbiyya. Allah ya sa mu dace, amin.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.