Kannywood Shirin Inada Hujja

87

- Advertisement -

Suna: Ina Da Hujja

Tsara labari: Munzali M Bichi

Furodusa: Abdulaziz Dan Small

Bada umarni: Ali Gumzak Sak

Kamfani: Global Time Mobies conjuction with Two by Two Bichi film producion.

Jarumai: Sadik S Sadik, Sadiya Adam, Hajara Usmn, Binta Kofar Soro, Shu’aibu Idris Lilisco, Malam Inuwa, M. Haruna Marhaba, Isma’il M Isma’il, Abdul A Buba

Fim din Ina da Hujja labari ne a kan wasu ma’aurata da su ke zaman lafiya tsakaninsu cikin kwanciyar hankali da soyyaya Musaddik (Sadik S Sadik) da Amal (Sadiya Adam) suna cikin zamansu kwatsam sai Amal ta sami ciki Musaddik ya buddidike akan cewar shi ba cikinsa bane duk da zaman aure da suke yi hakan ya yi matukar jefa Amal acikin tashin hankali domin tace ita bata taba sanin wani da namiji ba bayansa kuma Amal ta kafe akan kudirinta shima Musaddik ya kafe akan nasa kudirin, cin mutuncin yau da ban na gobe daban kullum haka, zaman lafiya ya kaurace musu sakamakon wannan ciki Musaddik ya tursasa Amal akan lallai sai ta fadi wanda ya yi mata amma Amal bata fada ba har sai da takai ya je ya sami mahaifiyarsa (Hajara Usman) ya yi mata bayanin halinda yake ciki ta kama shi ta fadan ya ya za’ayi matarsa ta sami ciki kuma yace ba nasa bane menene hujjarsa? Musaddik ya fara bata labarin accident din daya samu kwanakin baya a hanyar Kaduna a lokacin da aka kaishi asibiti likita ya tabbatar masa cewar bazai taba haihuwa ba domin yasami matsala kuma ko’a lokacin da Amal tace masa tana da ciki sai da ya kuma komawa wurin likitan ya sake aunashi ya sake tabbatar masa da cewa bazai sami haihuwa ba, mahaifiyar Musaddik tana gama jin zancen itama ta daga hankalinta akan baza ta yarda ba a kakabawa danta cikin da ba nasa ba daga nan Musaddik ya yanke shawarar zai mika Amal a kotu mahaifiyarsa ta bashi goyon bayan mika Amal kotun.

Ranar da Musaddik da Amal suka bayyana a gaban kotu Alkali ya tuhumi kowannensu akan ya fadi gaskiyar magana kowannensu ya kafe akan cewar shi akan gaskiyarsa yake shi kansa Alkali mamaki ya cika shi domin ya kasa gane mai gaskiya acikinsu a lokacin ya umarce su akan za suyi Li’ani ma’ana rantsuwa da Alkur’ani mai girma kowannensu ya amince akan zai yi Musaddik ya fara dauro alwala aka fara ta kansa ya yi rantsuwarsa cikakkiya kuma ya roki tsinuwar Allah mai girma idan har cikin Amal na sa ne bayan ya rantse har sau uku aka dawo kan Amal itama ta fara rantsuwar da Alku’anin tana shirin fadar tsinuwa akanta mahaifin Musaddik ya yi sauri ya tashi acikin kotun ya dakatar da ita ya fara bai wa kotu labarin shine ya hada kai da mai aikin Amal ta saka mata maganin barci ya yi mata fyade lokacin Musaddik ya yi tafiya a wannan fyaden ne ta sami ciki saboda ita Amal sam batamasan abinda ya faru ba, da jin wannan lamarin ya gigita duk wanda yake cikin kotun Alkali ya yankewa mahaifin Musaddik hukunci dai dai da shari’ar musulunci. Abubuwan Birgewa:

1- An yi amfani da kayan aiki masu kyau musamman camerar daukar hoto. 2- An yi amfani da suttura mai kyau a fim din da wurare masu kyau musamman gida je wanda duk sun dace da labarin.

3- Labarin ya yi ma’ana sosai sannan akwai darasi kuma ya tsaru sannan tun daga farko ya taho tiryan tiryan ba tare da ya karye ba har ya dire.

4- An nuna girman hukunci irin na cikin Alkur’ani mai girma akan cewar babbar mafita ce akan duk abinda ya shigewa musulmi duhu to akwai hukunci acikinsa wanda ya warwareshi sannan da tasirinsa akan duk wani musulmi. Kurakurai:

1- A cikin kotu mai kallo ya ji Alkali yana cewa mahaifiyar Amal shin kune iyayen Amal? zaku iya fadar halayyar Amal? kuma mai kallo ya ga mahaifiyar Amal ita kadai ce a tsaye amma Alkali yana fadar lamirin mutum biyu ko kuma ace mutane dayawa, shin Alkali mantawa ya yi ne? ko kuma shi mutum biyun yake gani ‘yan kallo ne suke ganin ta ita kadai? 2- Yakamata ace Alkali ya fadi hukuncin auren Musaddik da Amal a musulunce da kuma cikin da yake jikinta tun da mai kallo bai ga sanda ya sake ta ba.

3- A cikin kotu akwai wurin da aka sami matsalarbin daukar sauki muryoyin wasun su sun dinga yin kasa mai kallo baya ji sannan daga bisani aji ta dawo dai dai musamman muryar Musaddik.

4- Akwai wurin da Musaddik ya bai wa mahaifiyarsa takardar da likita ya bashi ta sakamako akan cear bazai taba haihuwa ba tana budewa ta rufe ta fara masifa sakwanin dubawar ta ta bai ci ace har ta karanta ba sannan result na asibiti likita ne yak gane abinsa domin ba rubutu ne na turanci kai tsaye ba akwai wasu formular da su suka sani domin sune suka karanta saboda aikinsu ne sannan kuma ba da hausa aka rubuta ba ballanta ta yi wannan saurin ganewar.

5- A cikin kotu akwai wurin da Musaddik yake baia Alkali labarin lokacin da yasami hatsari sanadin rashin haihuwarsa Boice ober din da akayi amfani da ita mai kallo yasan sam wannan muryar bata Musaddik bace.

6- An bar mai kallo acikin duhun illar da Musaddik ya samu sakamakon accident din da ya samu hara kai ga bazai iya haihuwa ba menene matsalarsa? idan ma abin ya yi girma yanda bazai fabu ba yakamata a sanya wata hikima wanda za’a gane kai tsaye ba tare da an fada ba.

7- Ta wacce hanya Mahaifin Musaddik ya kulla alaka da mai aikin gidan Musaddik da har ya kirata office dinsa?

8- Mai kallo kawai ya ga mahaifin Musaddik ya shigo gidansa kai tsaye ya tsaya a falo yana kallon matarsa ita kuma ta juya ta kalleshi ba tare da ta yi magana ba ta haye sama shin mai ya kawo shi gidan kai tsaye? Amal bata ga uban mijinta ba ta haye sama bata gaishe shi ba? menene makasidin aikata hakan? a gaske hakan bazata faru ba idan kuwa ta faru to tabbas yakamata ace an samar da dalili. Karkarewa:

Labarin ya sami tsari mai kyau kuma ya yi ma’ana amma an nuna wasu abubuwa wanda a gaske faruwarsu wahala ce sannan wani abin an barshi acikin duhu ba’a warware ba har din ya kare. Allahu a’alamu.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.