Matsalar Game Kqfafuwa Yayin Zama

144

- Advertisement -

Mafi yawancin mutane in suna zaune sukan harde kafafun kuma mutane da dama basu sane da illolin dake tattare da harde kafafunsu. Irin wannan harde kafar, gayu mata da kuma musamman manyan mata, sunfi yin hakan. Amma sai dai, mafi yawacin mutane da suke yin dabi’ar harde kafa, basu da masaniyar cewar yin hakan zai iya shafar kiwon lafiyarsu da kuma janyowa jikinsu illa. zakaga irin wannan zaman yana da gwanin sha’awa, kuma ba zama bane da aka sabada yinsa ba, amma ba’a son a harde kafar ya dauki tsawon lokaci. Ga mutanen da suke da kiba, kuma suka yi irin wannan zaman, zasuji dadi sosai a jijiyoyinsu ba, sabanin a yadda suka saba zama.

A cewar Dakta Fatai Adeniyi, kwararre akan sassan jikin mutane, dake Kwalejin hada magunguna a jami’ar , Ibadan cikin jihar Oyo, “ga masu kibar harda mutane marasa jiki, basa jin dadin irin wannan zaman”.

Dakta Adeniyi, ya ce, zama da kafafu a harde, yana sanyawa sashen jikin mutum ya kasance yana rike da kasusuwan jikin mutum don mikewar kafar domin mutum ba ya zauna bane a yadda ya saba ba. Yaci gaba da cewa, “irin wannan zaman, zai iya shafar yadda jini yake zagayawa a jikin mutum kuma akwai lokacin da jijiyoyin jinin dake jikin mutum zasu iyaya hadewa kuma jinin ba zai dinga gudana kamar yadda ya kamata ba.”

Daktan ya ce, irin wannan zaman, ana ganinsa kamar karamin abu a farko yinsa, amma zai iya haifarwa da lafiyar mutum matsala a nan gaba. Ya ce, shi yasa wasu mutanen sukan canza zamansu ta hanyar harde kafafunsu,inda suke kuma shinfida kwiwowinsu a kasa zuwa digiri tsa’in don suji dadin zama.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewar zama yadda ya kamata yafi kyau kuma yana kara hazaka da bayarda kariya daga kamuwa da ciwon baya da kamuwa daga cututtuka da kuma kare kamuwa daga ciwon siga.

Wani Likita na tuntuba akan sassan jikin dan adam dake Asibitin kwararru a garin Ibadan cikin jihar Oyo Dakta Abiodun Adeoye ya ce, daukar dogon lokaci kafa a harde yana janyo tafin kafa ya yi sanyi.

A cewar sa,”harde kafafu yana kuma dorawa jijiyon dake gwiwa nauyi kuma yana snayawa kafar dake kasa da tafin kafa nauyi, kuma hakan zai sanyawa mutum rashin kasa tafiya idan ya tashi.”

Ya ce ko da jinin mutum ya yi sanyi, ba a yarda da harde kafa ba domin yin hakan zai iya sanyawa jinin jikin mutum ya hau. Binciken da aka gudanar ya nuna cewar, harde kafa zai iya janyo ciwon hawan jini. A wani bincike da aka gdunar a wani Asibitin dake kasar Istanbul ya tabbatar da hakan kuma anyi hakan ne a bisa binciken da aka gudanar akan masu harde kafafunsu.

Bugu da kari jini yafi hawa ne idan aka harde kafa, amma idan aka auna tare da mai-maitawa zuwa mintuna uku, bayan an harde kafar, jinin dake cikin kafar yana sauka ya koma daidai. Yawan kamuwa da ciwon hawan jinin da ya auku akan mutane da suke harde kafafu su jima har tsawon wani lokaci ba tare da sun sauke kafar ba don ta samu ta huta.

Anyi hasashen cewar jinin dake cikin kafa yana samun mastala wajen zagayawa saboda harde kafa da kuma hana zuwan jini a cikin zuciya. Wannan yana sanywa jini ya karu zuwa cikin zuciya. Ya ce, sai dai, harde kafa akan gwiwa a lokacin da aka zauna bai janyo hawan jini, amma yana hana zagayawar jini ga mutanen da suke dauke da cututtuka.

Masu binciken lafiya baza su san cewar mutanen suna dauke da wannan matsalar ba. A cewar sa, wannan yana faruwa ne a cikin jijiyoyin jini kuma hakan yana haifar da jin gajiya ga kafa da kuma lokacin motsa jiki. Shi kuwa wani likitan tuntuba akan gyaran kashin baya, dake jihar Legas Dakta Tayo Ayorinde, ya ce, ba’a son wanda aka yiwa aikin kashin gadon baya ya dinga harde kafa. Ya ce sai dai, harde kafa akan gwiwa baya haifarwa da mutane ciwon sanyi na kafa.

Dakta Ayorinde ya bayanna cewar, “ a bisa iya ilimi na harde kafa baya janyo wata illa.” Ya ce, in har mata sun so su harde kafafunsu saboda wasu dalilai nasu, ya tabbatar da cewar kada su dauki dogon lokacin a yayin d asuke harde kafafun nasu. Yaja kunnen wadanda suke wuce shekaru arba’in akan harde kafa, musammna a lokacin da suka yi tafiya mai tsawo domin yin hakan zai sanyawa jinin yaki zagayawa kamar yadda ya kamata. Ya kara da cewa zaman ba wanda ba’a saba yinsa ba yana janyo kafar mutum tayi sanyi kuma zai iya sanyawa jini yaki zagaya wa kamar yadda ya kamata da daurewar jijiyiyoyin jikin mutum.

Kuma hakan zai iya janyowa lokacin da mutum yaso ya tashi ya kasa tashi tsaye. Ya bayar da shawara da a zauna kamar na tsawon mitin talatin da kuma mikar da da jiki sosai. Ya yi nuni da cewar, yawan mutuwar mutane yafi aukuwa ne ga mutanen da suka zauna har taswon minti talatin ba tare da suna mikar da kafarsu ba.

Ko da harde kafa baya haifar da ciwon hawan jini a nan gaba, wasu mutanen sun bayar da shawarar cewar zai haifarwa da jijiyoyin jin illa. Wani lokacin kananan jijiyoyi zasu iya samun matsala wajen tafiyar da jini yadda ya kamata kuma jijiyoyin zasu iya yin rauni.

Harde kafa zai iya janyowa kashin dake mara ya zauna ba’a yadda ya kamata ba. A saboda wannan daliin nbe zai iya shafar jijiyoyin dake cikin jikin mutum da kuma jijiyoyin dake waje na mutum. Hakan zai kuma iya janyowa hadakr kashin gwiwar mutum matsala.

A bisa wani binike da aka gudanar ya nuna cewar, mutanen da suke harde kafa da ya wuce fiye da awa uku za su iya fuskantar matsala a kafadar su.

- Advertisement -

Leave A Reply

Your email address will not be published.